| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
Paris Saint-Germain ta lashe gasar Champions League bayan ta lallasa Arsenal a bugun fanareti
Bayan an kasa samun wanda ya yi nasara a ƙarin lokacin da aka yi, PSG ta zama ƙungiya ta biyu da ta riƙe kambunta na lashe kofin.
Paris Saint-Germain ta lashe gasar Champions League bayan ta lallasa Arsenal a bugun fanareti
'Yan wasan PSG da koci Luis Enrique suna murna da kofin Zakarun Turai bayan sun doke Arsenal a wasan karshe na 2026 a Budapest.

Paris Saint-Germain (PSG) ta riƙe kambun Gasar UEFA sakamakon doke Arsenal 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan sun tashi 1-1 wasan karshe da suka buga a filin wasa na Puskas Arena ranar Asabar.

Arsenal ce ta fara samun nasarar zura ƙwallo ta hannun Kai Havertz a minti na shida, amma PSG ta farke bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, yayin da Ousmane Dembele ya jefa wa Arsenal ƙwallo a bugun fanareti a minti na 65.

A minti na 62, aka bai wa PSG bugun bayan Cristhian Mosquera ya kwarfe Khvicha Kvaratskhelia.

Dembele ya taso bayan minti uku, kuma cikin natsuwa ya kaɗa mai tsaron raga David Rayaa, inda wasan ya dawo kunnen doki.

Saura ƙiris Kvaratskhelia ya ƙara samar wa PSG nasara a minti na 78 bayan ya ja ƙwallo tun daga rabi har cikin yankin fanareti na Arsenal, amma ƙwallon da ya sharara ta daga turken raga sannan ta fita waje.

PSG ta ci gaba da matsawa neman nasara kuma ta sake kusantar nasarar a minti na 89 lokacin da Desire Doue ya bai wa Vitinha ƙwallo, inda kaɗan ya rage kaɗƙwallon da ya shimfiɗa ta shiga raga ta sama.

Dab da za a tashi kuma, Bradley Barcola ya ɓarar da wata babbar dama bayan an zari ƙwallon mayar da martani, inda ya ɓuga ƙwallo gefen raga bayan ya wuce ‘yan bayan Arsenal.

Da aka tashi wasan a haka, wasan ya ci gaba bayan ƙarin lokaci. Kungiyoyin biyu sun yi ta faman neman damar jefa ƙwallo cikin ƙarin mintuna 30, kuma a ƙarshe bugun fanareti ya raba gardama.

Jerin penalti sun yanke hukunci

An tantance wanda ya lashe kofin UEFA Champions League ne ta hanyar bugun fanareti.

Ga PSG, Goncalo Ramos da Desire Doue sun ci bugunsu na farko da na biyu. Viktor Gyokeres na Arsenal ya ci bugunsa na farko a bangarensa, amma Eberechi Eze ya ɓarar da bugu na biyu ta hanyar harba ƙwallon nesa da raga.

Ƙwallo ta uku ta PSG, da Nuno Mendes ya buga, mai tsaron raga Raya ya kama ta; hakan ta bai wa Declan Rice damar ci wa Arsenal ƙwallo ta uku aka dawo 2-2.

Achraf Hakimi ya ci wa PSG ƙwallo a bugu na huɗu , yayin da Gabriel Martinelli ya mayar da martani ya samar wa Arsenal asara aka dawo 3-3.

A bugun PSG na biyar, Lucas Beraldo ya ci ƙwallonsa ba tare da kuskure ba. Sai ɗan bayan Arsenal, Gabriel da ya taho yana fatan fitar da ƙungiyarsa ta Arsenal kunya, ya harba ƙwallon waje.

PSG ta samu nasarar jefa ƙwallaye 4-3 a bugun fanareti, inda ta lashe kofin UEFA Champions League.