Matashin ɗanwasan gaba na Monaco, Ansu Fati, ya zo da wani abin mamaki a duniyar ƙwallo, bayan da ya ƙaddamar da waƙarsa ta farko da ta saka shi cikin sahun mawaƙa.
Ɗanwasan ɗan shekaru 23 ya fitar da waƙa mai suna 'Sea como sea', bayan ya shiga kwantiragin sayar da waƙarsa tare da kamfanin Music Brokers, mallakin Sony Music.
Hakan ya mayar da Ansu Fati ɗanwasa na farko da ya halarci makarantar koyar da ƙwallon ƙafa ta Barcelona, wato La Masia, wanda ya shiga harkar waƙar ƙwararru.
Waƙar tsawonta minti biyu ne da sakan 15, kuma ta ƙunshi haɗakar raujin waƙar Afrobeats, reggaeton, da Amapiano.
Rahotani sun ce Fati ya fara shirya fitar da waƙa tun lokacin yana neman warakar da ya kwashe tsawon lokaci, bayan ya samu rauni a gwiwarsa a 2020.
Ya ɗauki kaka guda yana aiki cikin sirri tare da wani sutudiyon kiɗa a birnin Nice na Faransa, tare da wani fitaccen mai rikodin, Gambinoalaprod da kumatsohon ɗanwasan Faransa, Paul Pogba.
Wani abin birgewa shi ne, shugaban Music Brokers, Federico Scialabba, ya jaddada cewa Fati ƙwararren mawaƙi ne da yake gina hazaƙarsa a-sannu-a-sannu.
Ba wannan ne karon farko da ‘yanwasan ƙwallo ke amfani da waƙa wajen bayyana basirarsu ba.
Akwai irinsu tsohon ɗanwasan Barcelona, Jose Pinto, da taurari kamar Memphis Depay da Neymar da suke yin abu makamancin haka.










