| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun daƙile harin daren 'yanta'adda kan sansanin soji
Hukumomin soji a Nijeriya sun bayyana harin da aka daƙilen a matsayin wani muhimmin komabaya ga 'yanta'addan.
Dakarun Nijeriya sun daƙile harin daren 'yanta'adda kan sansanin soji
Tsohon Hoto: Dakarun NIjeriya na yaƙar 'yanta'adda a sassan ƙasar

Nijeriya ta ce dakarun tsaronta sunyi nasarar daƙile wani harin ta’addanci na cikin dare kan wani sansanin soji a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin ƙasar, inda suka kashe da yawa daga cikin maharan tare da ceto fararen hula 9 da aka yi garkuwa da su.

Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1:40 na dare ranar Lahadi, 2 ga watan Agusta, shekarar 2026, a sansanin sojin da ke Kasuwan Daji, cikin Ƙaramar hukumar Kaura Namoda .

Jami’an soji sun ce, dakarun da aka tura a ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma sun “gano tafiyar abokan gaba yayin da ‘yanta’addan suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin a ƙarƙashin duhun dare.”

Jami’ai da suke cikin shirin ko-ta-kwana sun mayar da martani da buɗe wuta da ya fi ƙarfin maharahan, lamarin da ya haddasa musayar wuta mai zafi da ya tilasta wa maharan watsi da abin da ya kai su kuma suka ja da baya cikin ruɗani.

Ceto waɗanda aka yi garkuwa da su

“Biyo bayan aranagamar ta farko, ƙarin sojoji sun iso kuma dakaru sun bi ‘yanta’addan da ke tserewa da suka riga suka saci wasu mazauna gundumomin da ke kusa yayin harin, da gudu,” kamar yadda rundunar sojin ta bayyana a wata sanarwa.

Yadda dakarun suka bi ‘yanta’addan da gudu ya ba da nasarar ceto mutum 9 da ke cikin mazauna yankin da aka yi garkuwa da su, kuma sojojin sun kuɓutar da su cikin aminci, in ji sanarwar.

Rundunar sojin ta kuma ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa ta intanet cewa an kashe jami’an tsaro shida a harin, inda ta bayyana cewa hafsan soji ɗaya tare da ɗansanda ɗaya ne suka mutu a harin.

Hukumomin tsaro sun bayyana harin da bai yi nasara ba a matsayin "wani ƙarin muhimmin komabaya na aika-aika ga ‘yanta’addan ," suna masu cewa lamarin ya haddasa gagarumar asara ga ƙungiyoyin ‘yanbindiga a ƙarshen makon.