| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
An kashe wasu 'yanta'adda tare da kama mutum 22 masu taimaka wa masu aikata laifuka a Nijar
Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ce an yi wannan ne tsakanin ranar 3 zuwa 8 ga watan Maris.
An kashe wasu 'yanta'adda tare da kama mutum 22 masu taimaka wa masu aikata laifuka a Nijar
jamhuriyar Nijar da sauran ƙasashen yankin na fama da hare-haren 'yanta'adda / ANP

Dakarun tsaron Nijar (FDS) sun kashe wasu ‘yanta’adda tare da kama masu haɗa baki da masu aikata laifuka 22 a cikin mako ɗaya.

Wani harin bam da sojoji suka kai wajen garin Kokorou ya rutsa da wasu ‘yanta’adda da ke safarar dabbobin da suka ƙwace daga mutane.

Harin ya kashe biyar daga cikin ‘yanta’addan kuma binciken da aka gudanar kan gawarwakinsu ya sa an gano kayayyakin soji daga gare su, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ANP ya ruwaito.

Kazalika a lokacin samamen sojojin sun ƙwace shanu da suka kai 103 daga ɓarayin kuma suka mayar wa waɗanda aka sace daga gare su.

ANP ya ruwaito cewa ranar 4 watan Maris dakaru sun kashe wani ɗanta’addan a garin Torodi a yammacin ƙasar.

Dakarun Operation Niya sun ga mutumin kusa da kayayyakin soji ne a garin inda yake ƙoƙarin tattara bayanai game da abin da ake ganin shiri ne na kai hari kan dakarun tsaron ƙasar, kuma da ya yi ƙoƙarin tserewa sai a ka harbe shi, in ji ANP.

Kazalika an gano wani mutum da aka bayyana a matsayin mai kwarmata bayanai ga ‘yanta’adda a wani shingen binciken soji da ke Samira yayin da yake ƙoƙarin tattara bayanai.

Nan take aka kama shi kuma aka kashe shi, in ji rahoton na ANP.

Bincike kan kayayyakinsa ya sa an gano wayar salula ƙirar Motorola da sauran abubuwan da ke nuna alaƙarsa da aikata laifuka.

Bayan kwanaki biyu, wata tawagar jami’an tsaro ta Makalondi ta je wajen Bankata Gourmantché, inda ta lalata dukkan kayayyakin ‘yanta’adda na jigilar kayayyaki waɗanda wasu daga cikinsu za a yi amfani da su wajen haɗa bam.

Rahoton ya ƙara da cewa an ƙwace ababen haɗa bam da yawa a wannan samamen kuma nan take aka lalata su.

Kazalika rahoton ya ce dakarun Operation Garkouwa sun yi nasarar kama masu wata motar dakon mai na masu safarar mai inda suka kama litar man gas 46,000.

Baya ga ‘yanta’addan da dakarun suka yi nasarar kashewa, ayyukan da suka yi a cikin wannan lokacin ya sa dakarun sun yi nasarar kama mutum 22 ciki har da masu haɗa baki da masu aikata laifuka.

Rumbun Labarai
Kotun Nijeriya ta hana ’yanjarida halartar zaman shari’ar mutanen da ake zargi da shirya juyin mulki
'Yanbindiga sun kai hai wani gidan marayu a Jihar Kogi sun sace yara 23 amma an ceto 15
Jakadan Saudiyya a Nijeriya ya gana da Dangote don inganta kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu
Shugaban Nijeriya ya nuna goyon baya ga kasashen Gulf game da yaƙin Iran
Babbar Alƙaliyar Nijeriya ta gargaɗi kafafen yaɗa labarai da su guji ƙarin gishiri a rahotanni
Tinubu ya nemi izinin majalisar dattawan Nijeriya don karɓo bashin $516m a gina titin Sokoto-Badagry
Tinubu ya cim ma yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama domin hana shirinsu na dakatar da aiki
Sojojin Nijeriya sun kashe mayakan ISWAP da dama a yankin Tafkin Chadi
Aƙalla mutum 23 ‘yanta’adda da ‘yanbindiga suka kashe a hare-hare daban-daban a arewacin Nijeriya
CBN ta gargadi 'yan Nijeriya kan yunƙurin masu kutse cikin asusun bankunan mutane
Dimokuraɗiyya za ta ɗore duk da barazanar da take fuskanta – Tinubu
An samu bullar Covid-19 a Nijeriya shekaru bayan duniya ta yi fama da ita
Tinubu ya sauke Ministan Kuɗi Edun Wale Edun da na Gidaje Ahmad Dangiwa ya ba da sunan wasu sabbi
Sojojin saman Nijeriya sun kashe tarin 'yan-ta'adda a dajin Sambisa
Nijeriya za ta gurfanar da janar mai ritaya da tsohon minista a kotu kan tuhumar su da juyin mulki
A karon farko Nijeriya ta fitar da mai fiye da wanda ta shigar cikin ƙasar
Dakarun Nijeriya sun kama masu kai wa 'yanta'adda makamai a Jihar Kogi
Dalilai uku na ɗage shari'ar tabbatar da Sarkin Kano a Kotun Ƙolin Nijeriya
NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin kwanon abinci a filin jirgin saman Legas
Farashin saniya ya kai naira N2.5m, fiye da farashin mota a Legas, in ji mahauta