A wannan makon, yayin da Shugaba John Dramani Mahama na Ghana ke ziyara a Lusaka, an cimma wata yarjejeniya mai sauƙi a fili: Ghana da Zambia za su soke amfani da biza a tsakaninsu.
Ga masu kallon wannan lamarin da shakku, za a iya ɗaukar hakan a matsayin ƙaramar magana ta diflomasiyya.
Amma ni na ke cewa wannan aiki ne mai ƙarfi, mai tattare da sauyi, kuma cike da siyasa. Ba wai tafiya kawai ake magana, fattaka ce kai tsaye kan wani tsarin da aka jima ana fama da shi wanda Turawan mulkin mallaka suka gadar mana a Afirka: wato tsarin rashin yarda da ‘yan uwanmu.
Tsawon shekaru, babbar matsala ga rajin kishin Afirka ba matsala ba ce ta harshe, nisa da juna ko al’adua. Ita ce jami'in shige da fice a filin jirgin samanmu.
Farkon haduwar 'yar kasuwa Ghana ko wani malamin makarantar Zambiya batu ne kawai na bincike, shakku da kuma aika saƙon cewa akwai yiwuwar kai matsala ce, ko kuma wanda zai tamaka wurin haddasa ta ba.
Mun kafa waɗannan shingen ne da sunan tsaro da ikon mallaka, amma muka bar ƙofofi a buɗe ga waɗanda ke son amfani da su.
Abin baƙin ciki da alamar rashin adalci shi ne: Mai yawon bude ido daga Turai sau da yawa zai iya zagaya nahiyarmu cikin sauƙi fiye da ɗan kasuwar Afirka.
Mun tsara tsarin da ke kallon 'yan uwa a matsayin barazana, yayin da muke shimfiɗa jan kafet ga masu buƙatu da suka daɗe suna kwasar arzikinmu.
Gina hanyoyin haɗin kai na asali
Saboda haka, yarjejeniyar Ghana‑Zambia ta wuce yarjejeniya ta sauyin tsare-tsare. Ta zama ta sauya tsarin yadda ake kallon abubuwa.
Ta bayyana cewa ɗan ƙasar Afirka ba hadari bane kai tsaye. Ta amince cewa kwararar mutane cikin sauƙi shi ne ƙashin bayan kasuwanci, al'adu, da musayar ilimi.
Ka yi tunanin abin da hakan zai iya haifarwa: mai kirkirar fasaha daga Accra zai iya yin haɗin gwiwa ba tare da matsala ba da ƙwararren aikin makamashi mai tsafta a Lusaka.
Mai shirya fim daga Kitwe zai iya tara ma'aikatan fim daga Tamale ba tare da jiran izinin tafiya mai cin rai ba.
Haka nan wannan yana nufin gina cibiyoyin haɗin kai masu asali, masu juriya, kuma marasa dogaro da izinin tsoffin ƙasashen mulkin mallaka.
Duk da haka, yaba wa wannan mataki ba tare da la'akari da muhallin sa ba zai sa mu rasa nauyin juyin juya hali da ke tattare da shi.
Dole mu tuna cewa Ghana da Zambia ƙasashe ne da aka haɓaka cikin wutar gwagwarmayar kawar da mulkin mallaka.
Kwame Nkrumah da Kenneth Kaunda ba su yi yaƙi don 'yanci ba domin jikokinsu su buƙaci biza don musayar ra’ayi a fadin nahiyar. Sun yi mafarkin Afirka da ba ta da iyaka, wuri na gaskiya na 'yanci inda mutane za su iya karɓar duka gadonsu.
Soke biza ƙaramar hanya ce ta zahiri ta dawo da wannan mafarki wanda aka sace. Wata ƙin yarda ce ga taswirar rarrabuwa da aka tilasta a Taron Berlin na 1884, taswira da muka ɗauka a ciki har muka fara kula da ita kamar ƙa'ida.
Sharuɗɗan nasara
Amma ainihin gwaji yana gaba. Kawar da biza shi ne mafi sauƙi. Aikin da ya fi wahala kuma ya fi muhimmanci shi ne gina ababen more rayuwa na tattalin arziki da na zamantakewa waɗanda za su ba wannan 'yanci ma'ana.
Me ne amfanin buɗe iyakoki idan kuɗinmu ba za a iya musanya su ba, idan hanyoyin kasuwanci sun lalace, kuma idan kasuwanninmu ana saka shinge tsakaninsu amma a buɗe domin jibge kayayyakin ƙasashen waje?
Wannan matakin diflomasiyya ya zama harshen wuta da zai samar da jerin ayyuka masu cike da goyon baya:
Tsare‑tsaren kasuwanci da suka daidaitu: Muna bukatar amincewar juna kan cancantar ƙwararru, sauƙaƙe rajistar kasuwanci, da yarjejeniyoyin kauce wa biyan haraji sau biyu waɗanda za su sa harkokin ƙetare iyaka su zama masu sauƙi.
Zuba jari a haɗin kai: Ba kawai jigilar jiragen sama ba, har ma da tsarin biyan kuɗi na dijital mai sauƙi da arha da kuma ingantacciyar hanyar sadarwa ta yanki don ba da damar haɗin gwiwar da wannan motsin maras biza zai haifar.
Sauyin labari: Dole ne kafofin watsa labarai da tsarin iliminmu su rinƙa nuna nasarorin labaran Afirka, su bar tsarin da ke nuna ilimi na da muhimmanci ne kaɗai daga ƙasashen Yamma.
Shugaba Mahama da Shugaba Hichilema sun yi wani abu mai muhimmanci. Sun canza ƙa'ida. Amma babban ƙalubale shi ne canza gaskiya.
Mafarkin fasfo ɗaya na Afirka
Sun cire kwaɗo; yanzu wajibi ne mu gina birni mai walwala a bayan ƙofar. Wannan magana ce ta sauya tunaninmu game da tsaro daga wanda ya dogara da hana mutane shiga zuwa wanda ya dogara da wadata da haɗin kai da ke fitowa daga bari mutane su shiga.
Bari wannan ya zama kyakkyawan misali mai yaduwa. Allah Ya sa ya bazu daga hanyar Zambia zuwa Ghana zuwa kowace kusurwa ta nahiyarmu.
Domin idan dan Afirka zai iya tashi a Lagos, ya yi taron rana a Nairobi, ya kuma kammala ciniki a Johannesburg, duk da fasfo guda ɗaya kuma ba tare da wata shaida ta cin zarafin birokrasiya ba, za mu fara gina sabon tsarin daraja.
Wannan ita ce Afirka da ake so mu gada. Wannan ita ce Afirka da dolen mu, da ƙarfin hali da manufofi mu gina ta a ƙarshe.
Marubucin, Kennedy Chileshe, shi ne Daraktan Zartarwa na Jubilee Leaders Network, wata ƙungiya mai fafutukar manufofi da jagoranci.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba lallai su yi daidai da ra'ayoyi, manufofi ko tsarin shirye‑shiryen editoci na TRT Afrika ba.
















