| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Mutane fiye da 4,000 ne suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo - Gwamnati
Masana sun yi nuni kan jinkirin gano cutar da wuri da yawan sa ido da kuma rikicin sojoji a matsayin wasu daga cikin abubuwan da suka kawo cikas ga kokarin dakile yaduwar cutar.
Mutane fiye da 4,000 ne suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo - Gwamnati
Fiye da mutane 62,000 ne suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

Adadin wadanda suka kamu da cutar Ebola da aka tabbatar a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya zarce fiye da mutum 4,000 a karon farko tun bayan ɓarkewar cutar a baya bayan nan, a cewar bayanan gwamnati.

An bayyana annobar, wacce ita ce ta biyu mafi girma a duniya, a matsayin wadda ta fi yaɗuwa a cikin sauri a tarihi.

Ƙwararru sun yi imanin cewa sai da cutar ta fara yaɗuwa watanni kafin a ayyana ta a matsayin annoba a ranar 15 ga Mayu kuma adadin waɗanda suka kamu da cutar na iya zarce wanda aka fitar a hukumance.

A wani sabon rahoto da ta fitar, Cibiyar kula da Lafiyar Jama’a ta ƙasar da ke yankin Afirka ta Tsakiya ta ce jimillar waɗanda suka kamu da cutar ta kai mutum 4,053, ciki har da mace-mace 1,850.

Yaɗuwar cutar a faɗin ƙasar

An samu ɓullar cutar a larduna biyar na ƙasar: waɗanda suka haɗa da Ituri da Arewacin Kivu da Kudancin Kivu da Haut-Uele da kuma Tshopo.

Wani rahoto da mujallar Science ta wallafa a watan jiya, ya bayyana cewa tun daga watan Janairu ko baya ga haka aka samu ɓarkewar Ebola a lardin Ituri na ƙasar Kongo.

Kazalika, masu bincike sun gano fiye da mutane 500 da ake tsammani sun kamu da cutar tsakanin tsakiyar watan Janairu zuwa 15 ga Mayu.

Masana sun yi nuni kan Jinkirin gano cutar da yawan sa ido da rikicin sojojin da rashin karɓar alluran rigakafi da magungunan nau'in ƙwayar cutar sun sanya ƙoƙarin da ake yi wajen daƙile cutar ya ci tura a wannan karon.

Ya zuwa yanzu, ɓarkewar cutar a yankin Yammacin Afirka tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016 ce kawai ta zarce na yanzu, inda aka samu fiye da mutane 28,000 a ƙasashen Guinea da Laberiya da kuma Saliyo.