Ukraine ta harba wa Rasha makami mai linzamin ATACMS da aka kera a Amurka yayin da yaki ya tsananta
Garkuwar tsaro ta Rasha ta tare makamin mai linzami na Ukraine mai tsananin gudu da aka harba shi zuwa birnin Voronezh, inda aka dakile ta'adinsa, yayin da ya lalata wasu gine-gine.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce sojojin Ukraine sun harba makamai hudu masu linzami na ATACMS da Amurka ta kera a kan birnin Voronezh na kudancin Rasha a ranar Laraba, a yunƙurin kai hari kan fararen hula.
A ranar Talata, rundunar sojin Ukraine ta bayyana cewa ta kai hari kan cibiyoyin soja a cikin Rasha da makaman ATACMS da Amurka ta ba ta, tana kiran hakan a matsayin “muhimmin ci-gaba.”
Kiev ta karɓi waɗannan makaman a 2023, amma a farko an takaita amfani da su ne kawai a kan yankunanta, waɗanda kusan kashi ɗaya cikin biyar na yankuna ke hannun Rasha.
"Tsarin tsaron sama na Rasha na S-400 da Pantsir sun kakkaɓo dukkan makaman na ATACMS," in ji ma’aikatar tsaron a Telegram.
Ɓurbushin da suka fado daga makaman da aka tare sun lalata rufin wani gidan gajiyayyu da ke Voronezh da wani gidan marayu, haka kuma sun lalata wani gida daya, in ji ma’aikatar, tare da ƙara da cewa babu asarar rai ko raunuka ga fararen hula.
Ma’aikatar ta wallafa hotunan ƙananan ɓurɓushin makaman kuma ta ce tsarin tsaron sama ya gano cewa an harbo makaman na ATACMS ne daga yankin Kharkiv.
Rasha ta ce ta harba makaman Iskander-M don tarwatsa na'urorin harba rokoki masu yawa guda biyu na Ukraine.
A baya a watan Janairu, Ukraine ta kai hari a wasu yankunan Rasha da makaman ATACMS na Amurka, inda ta harba makamai shida zuwa yankin Belgorod na Rasha.
Bayan Ukraine ta harba makaman na ATACMS na Amurka da makaman Storm Shadow na Biritaniya cikin Rasha a bara, Putin ya umarci a harba makamin linzami mai gudun tsiya zuwa Ukraine.
Rasha ta ƙara tsananta hare-hare kan Ukraine
Wani harin jiragen sama marasa matuka da aka kai da daddare sun raunata aƙalla mutane 36 a Kharkiv, ciki har da yara biyu, in ji Gwamnan Oleg Synegubov a ranar Laraba.
Jiragen sama marasa matuka goma sha ɗaya sun yi lugude a gundumomin Slobidsky da Osnoviansky, suka haifar da gobara a wani gini mai hawa tara kuma suka lalata motoci, da gareji da wata babbar kasuwa.
Ma’aikatan ceto sun kwashe mutane 48 daga wurin, yara biyu 'yan shekaru tara da 13 sun kasance cikin wadanda suka ji rauni, a cewar 'yan sanda, tare da ƙarawa da cewa likitoci sun gano cewa yaran suna da cikin mummunan yanayi na damuwa.
Moscow ta ƙara tsananta hare-hare kan ababen samar da makamashi na Ukraine, wanda ya zama farmaki mafi girma kan tashoshin gas tun watan Oktoba.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy na zagaya Turai yana neman tallafi ga rundunar Ukraine da kare muhimman kayan more rayuwa yayin da hunturu ke karatowa aka kuma gaza cim ma tattaunawar zaman lafiya.
Sojojin Ukraine, waɗanda suka gaji kuma ba su da yawa, suna ci gaba da kare bangaren gabas, yayin da rundunar Rasha ta kwace ƙauyuka biyu a ranar Talata.