| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya ta yi Allah wadai da hare-haren ta’addanci da aka kai a kasar Mali
Hukumomi a Mali sun bayyana cewa dakarun soji sun shawo kan lamarin biyo bayan wasu hare-hare da aka kai a jere kuma a lokaci guda.
Turkiyya ta yi Allah wadai da hare-haren ta’addanci da aka kai a kasar Mali
Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi Allah wadai da harin ta'addanci a Mali / TRT World and Agencies

Kasar Turkiyya ta yi Allah wadai da jerin hare-haren ta’addanci da aka kai a sassan ƙasar Mali, inda ta bayyana su a matsayin hare-hare na “rashin imani.”

An ba da rahoton jin ƙarar bama-bamai da kuma harbe-harben bindiga a safiyar ranar Asabar a wurare da dama, ciki har da kewayen babban birnin ƙasar wato Bamako, da Gao da Kidal da ke arewa, sannan da birnin Sévaré da ke tsakiyar ƙasar.

Rundunar sojin Mali ta ce an “shawo kan lamarin,” kuma “kungiyoyin ’yan ta’adda” da suka kai hari wurare daban-daban, ciki har da barikin sojoji, sun ɗanɗana “kuɗarsu.”

Waɗannan hare-hare sun janyo kakkausar suka, inda Turkiyya ta nuna goyon bayanta ga ƙasar wacce take yankin Afirka ta Yamma.

“Muna yin Allah wadai da hare-haren ta’addanci da suka faru a yau (25 ga Afrilu) a yankuna daban-daban na Mali. Muna roƙon rahamar Allah ga waɗanda suka rasa rayukansu a waɗannan munanan hare-hare, sannan muna mika ta’aziyyarmu ga ’yan uwansu da kuma al’ummar Mali baki ɗaya,” in ji ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar da yamma.

“Za mu ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da Mali a yaƙin da take yi da ta’addanci, da kuma tallafa wa ƙoƙarinta da nufin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin,” in ji sanarwar.

‘Murƙushe masu kai hari’

Rundunar sojin Mali ta yi kira ga ’yan ƙasa da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, inda ta ce “dakarun tsaro da na kare kasa suna nan cikin shiri wajen ganin sun murƙushe maharan.”

Wata ƙungiyar ta’addanci mai alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kai hare-haren, inda ta ce ta ƙaddamar da su ne a matsayin wani aiki na haɗin gwiwa da ’yan tawayen Abzinawa. Ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ko suka ji rauni ba.

Ƙasar Mali na fama da rashin tsaro tun daga shekarar 2012, inda ƙungiyoyin ta’addanci na Al-Qaeda da Daesh ke kai hare-hare kan sojoji da fararen hula.

Ƙasar wadda take yankin Afirka ta Yamma tana kuma fuskantar daɗɗiyar fafutukar ɓallewa da ’yan tawayen Abzinawa ke jagoranta a yankin arewa.

Ɗaya daga cikin wuraren da hare-haren na ranar Asabar ya shafa shi ne birnin Kati, wato mahaifar shugaban mulkin rioƙn ƙwarya na ƙasar, Assimi Goïta, wanda yake kan mulki tun bayan juyin mulkin soja a shekarar 2020.