Gomman ‘yanta’addan Boko Haram ne aka kashe ranar Asabar a wani jerin hare-haren sama da aka kai kan wuraren ɓuyar ƙungiyar a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya, in ji rundunar sojin saman ƙasar.
Mai magana da yawun rundunar sojin saman ƙasar Ehimen Ejodame ya bayyana hakan ne a wata sanarwa inda ya bayyana cewa an ƙaddamar da samamen ne a yankin Yaganari.
Ejodame ya ce gomman ‘yanta’adda ne aka kashe yayin da saura suka tsere da raunuka.
Ya ce an lalata wuraren ɓuyan ‘yanta’adda a hari saman yana mai ƙarawa da cewa an ƙwace bamaba-bamai da aka haɗa da hannu da makamai masu yawa a lokacin samamen.
"Kafin a kai hare-kare kan wuraren, bayanan da aka tattara ta sama sun tabbatar da cewa akwai kayayyakin ‘yanta’adda da cibiyoyin sufurinsu a wurin," in ji Ejodame.
Ya bayyana aikin a matsayin wata muhimmiyar nasara cikin yaƙin da ake yi da ta’addanci, yana mai cewa lamarin ya ƙara raunana ikon ‘yanta’addan na iya taruwa da kuma tafiya yadda suke so.
Tun farkon shekarun 2000 ne Boko Haram ta fara aika-aika. Gomman dubban mutane ne aka kashe a hare-haren ta’addanci da ƙungiyar ta ƙaddamar tun shekarar 2009.
Tun shekarar 2015, ƙungiyar ta kuma ƙaddamar da hare-hare kan ƙasashe maƙwabta, Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar. An kashe aƙalla mutum 2,000 a hare-haren Boko Haram a faɗin tafkin Chadi.
Ɗaruruwan dubban mutane ne hare-haren ta’addanci da tashe-tashen hankali suka raba da muhallinsu a yankin.












