Rundunar ’Yansandan Nijeriya tare da haɗin gwiwar Hukumar ‘Yansandan Ƙasa da Ƙasa INTERPOL, da ke Abuja ta kama tare da tasa ƙeyar wani ɗan ƙasar China da ake nema ruwa-a-jallo zuwa ƙasarsa domin fuskantar tuhuma kan safarar namun daji masu fuskantar barazanar ɓacewa.
Wanda ake zargin, Cai Jinlian mai shekara 42, na fuskantar zargin safarar kimanin tan 12 na kwanson dabbar ɗan-kunya daga Nijeriya zuwa China a jigila biyu da ya yi tsakanin Nuwamban 2018 da Afrilun 2019.
A cewar rundunar, binciken da Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Kwastam ta Wenzhou ta gudanar ne ya gano wannan laifi. An kuma gurfanar da wasu abokan aikinsa biyu, inda wata kotu a Wenzhou da ke lardin Zhejiang ta yanke musu hukuncin ɗaurin fiye da shekara 14 a watan Disamban 2020.
Bayan ya tsere daga China zuwa Masar a ranar 12 ga Yulin 2019, hukumomin ƙasar China suka samu sammacin kama shi a ranar 24 ga Maris, 2020, sannan INTERPOL ta fitar da sanarwar neman kama shi a ranar 10 ga Mayun 2020.
Binciken sirri daga baya ya gano cewa Jinlian ya koma Nijeriya a kusan shekarar 2023, inda ya riƙa zirga-zirga tsakanin jihohin Delta da Filato.
Bisa sahihan bayanan sirri, jami'an INTERPOL a Abuja sun kama shi a ranar 18 ga Yulin 2026, kafin daga bisani a mayar da shi birnin Shanghai na ƙasar China a ranar 29 ga Yulin 2026, ƙarƙashin yarjejeniyar haɗin gwiwar hukumomin 'yansanda tsakanin ƙasashen biyu domin ya fuskanci tuhumomin da ake masa.
Babban Sufeton ’Yansandan Nijeriya, Olutunji Rilwan Disu, ya yaba da ƙwarewa da jajircewar jami'an INTERPOL a Abuja wajen gudanar da wannan aiki cikin nasara.
Ya kuma umarci Sashen Yaƙi da Laifukan Muhalli da Kayan Tarihi na rundunar da ya ƙara ƙaimi wajen amfani da bayanan sirri domin yaƙi da safarar namun daji da sauran manyan laifukan da suka shafi ƙasashe da dama.
Disu ya sake jaddada kudurin Rundunar ’Yansandan Nijeriya na ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro na ƙasa da ƙasa ta hanyar INTERPOL da sauran abokan hulɗa domin yaƙi da manyan laifuka na ƙetare da kuma kare namun daji masu fuskantar barazanar ɓacewa.


















