Adadin jama'ar Turkiyya ya kai miliyan 86 a 2025 yayin da jama'ar ƙasar ke ƙara yawa
Maza sun kasance mutane miliyan 43.06 ko kashi 50.02 cikin ɗari na jumullar adadin, yayin da mata suka kasance kashi 49.98 ko mutane miliyan 43.03 a bara, in ji hukumar kididdiga TurkStat a ranar Litinin.
Yawan mutanen Turkiyya a shekarar 2025 ya ƙaru da 427,224 daga shekarar da ta gabata zuwa mutane miliyan 86.09, a cewar bayanan hukuma.
Maza sun kasance mutane miliyan 43.06 ko kashi 50.02 cikin ɗari na jumullar adadin, yayin da mata suka kasance kashi 49.98 ko mutane miliyan 43.03 a bara, in ji hukumar kididdiga TurkStat a ranar Litinin.
Matsakaicin ƙididdigar haɓakar yawan jama'a na shekara-shekara ya ƙaru zuwa biyar cikin dubu (5‰) a 2025, daga 3.4 cikin dubu (3.4‰) a 2024.
TurkStat ta ce: "Yawan mutanen da ke zaune a cibiyoyin lardi da ƙananan hukumomi, wanda ya kasance 93.4 cikin ɗari a 2024, ya zama 93.6 cikin ɗari a 2025. Bugu da ƙari, yawan mutanen da ke zama a ƙauyuka da ƙananan garuruwa ya ragu zuwa 6.4 cikin ɗari daga 6.6 cikin ɗari."
Istanbul, babban birnin kasuwanci na Turkiyya, shi ne birni mafi yawan jama'a da mutane miliyan 15.75, inda ya ƙaru da mutane 52,451 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Wanda ke biye da birnin shi ne birnin Ankara da mutane miliyan 5.9, sai birnin Aegean na Izmir da mutane miliyan 4.5, sai cibiyar masana'antu ta Bursa da mutane miliyan 3.26, da wurin shakatawa na gabar Bahar Rum Antalya da mutane miliyan 2.77.
Matsakaicin shekarun jama'a a Turkiyya ya tashi zuwa 34.9 a 2025 daga 34.4 a 2024.
Jumullar shekarun yara ‘yan ƙasa da shekara 18 da tsofaffi ‘yan shekara fiye da 64 kuwa , ya ragu da kashi 46 cikin ɗari a bara, raguwa da maki 0.1 na kashi.