| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Rundunar sojin Chadi ta ce an kashe jami'anta 23 a wani harin Boko Haram
Bayan harin Oktoban 2024, Shugaba Deby ya ƙaddamar da harin fansa inda ya sha alwashin jan ragama "shi da kansa" don kai hari tsawon makonni biyu.
Rundunar sojin Chadi ta ce an kashe jami'anta 23 a wani harin Boko Haram
Tafkin Chadi ya zama wata matattara ta mayaƙa 'yan-ta'adda / Reuters

Wani hari da aka kai cikin dare da ake zargin 'yanta'addar Boko Haram ne suka kai a wani sansanin sojojin Chadi ya halaka aƙalla mutum 24, a cewar wani jami’in soji ranar Talata.

Jami’in sojin yankin ya faɗa wa kamfanin dillacin labaria na AFP cewa harin ya faru ne a sansanin soji na Barka Tolorom da ke gaɓar Tafkin Chadi, mai iyaka da Kamaru, Nijar, da Nijeriya.

Majiyar ta gaya wa AFP cewa farmakin ya faru ne a daren Litinin, kuma ya "bar mutum 25 a mace, da kuma mutum 46 da raunuka a ɓangaren sojin Chadi".

Jami’in da aka zanta da shi ya ambaci "kisan mutum 24 da kuma tarin masu raunuka."
Duka majiyoyin sun ɗora alhakin harin kan Boko Haram, inda jami’in ya jaddada cewa "lamura sun lafa."

Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno ya wallafa a Facebook ranar Talata cewa, "Ta kuma faruwa, ƙungiyar ta’adda ta Boko Haram ta ƙaddamar da hari a daren jiya kan sansanin sojinmu a Barka Tolorom".

Ya sha alwashin cewa, "Za mu ci gaba da yaƙi da jaddada aniya har sai wannan barazanar an kau da ita gabaɗaya”. Sannan shugaban ya miƙa saƙon ta’azaiyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa.

Ƙaruwar hare-hare

Ana samun ƙaruwar farmaki kan sojoji daga Boko Haram a yankin Tafkin Chadi, inda wani hari na Oktoban 2024 ya halaka mutum 40 cikin rukunin sojin Chadi.

A watannin baya-bayan nan an samu ƙarin ƙaimi a hare-haren rassan ƙungiyar ta’adda ta JAS, har da satar mutane da hari kan tawagogin soji, musamman kan tsibirai da ke gaɓar tafkin da ke yankin Nijar.

Bayan wancan harin na Oktoban 2024, Shugaba Deby ya ƙaddamar da harin fansa inda ya sha alwashin jan ragama "shi da kansa" don kai hari tsawon makonni biyu.

Lokacin da harin fansar ya zo ƙarshe a Fabrairun 2025, rundunar sojin Chadi ta ce babu sauran "maɓoyar [Boko Haram] a iyakokin Chadi."

Tsibiran da ke cikin Tafkin Chadi ya zama wata mafaka ta mayaƙan Boko Haram da sauran gungun ‘yan-ta’adda da suka addabi yankin, ciki har da wani ɓurɓushin Boko Haram na ISWAP.

Rumbun Labarai
Me samar da lantarki ke nufi ga Afirka?
Chivayo: Rayuwar attajirin da ya mutu, wanda ya taba ba wa wani mawaki $1m don yin wasa a biki
Hare-haren 'yanta'adda sun kashe gomman sojoji a wurare biyu a Nijar
An zaɓi matasan Nijar 500 domin samun horo a kyauta don koyon sana’o’i a Aljeriya
Fiye da mutum 55,000 daga Sudan sun tsere zuwa gabashin Chadi don gudun hijira
Wasu karin mayakan RSF sun sauya sheka zuwa Rundunar Sojin Sudan bayan sun gamu da 'masifu'
Ana samun ƙaruwar Ƙasashen Yamma masu goyon bayan biyan diyyar cinkin bayi: Ghana
Shugaban Sudan ta Kudu Kiir ya rusa gwamnatin haɗin kan ƙasar
Zakuna goma sun mutu a wani gandun dabbobi da ke Tanzania
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi da lalata motocin yaƙin RSF
An kama mutum 10 ciki har da jami’an kwastam 4 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Ghana
Rundunar Operation Damissa a Nijar ta lalata maɓoyar mayaƙan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Dosso
Shugaban Nijar Tiani ya sauya wasu ministocinsa
Shugabar Majalisar Dokokin Cabo Verde ta zama shugabar ƙasar ta riƙo
Harin ta'addanci ya yi ajalin sojojin Mali aƙalla 50, da sojojin haya na Rasha biyar
Ƙasashen Afirka biyar sun kawar da yaɗuwar cutar shan inna, amma ba a gama yaƙin ba
Nabil Neghiz ya zama kocin tawagar Mena ta Nijar
Fiye da mutum 7,000 sun kamu da annobar Ebola a Jamhuriyar Kongo
Shugaban Nijar ya naɗa Birgediya Janar Mamane Sani Kiaou a matsayin sabon shugaban hafsan sojoji
FIFA ta musanta iƙirarin Maroko na 'karɓar baƙuncin' wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na 2030