| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Israila na ci gaba da kawo cikas ga duk wani ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Iran: Erdogan na Turkiya
Isra'ila ta nuna cewa 'tana amfanar da kanta daga tashin hankalin' ta hanyar rufe Masallacin Ƙudus, da neman hukuncin kisa ga Falasɗinawa fursunoni, da ƙara tashin hankali a Lebanon da Siriya.
Israila na ci gaba da kawo cikas ga duk wani ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Iran: Erdogan na Turkiya
Israila na ci gaba da kawo cikas ga duk wani ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Iran: Erdogan na Turkiya / AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce yakin da ya fara a ranar 28 ga Fabrairu a Gabas ta Tsakiya yana ci gaba da kashe mutane duk da ƙoƙarin diflomasiyya, yana zargin Isra'ila da daƙile matakan da ake ɗauka don kawo ƙarshen rikicin.

Bayan wani taron Majalisar Zartaswa a Cibiyar Fadar Shugaba a Ankara a ranar Litinin, Shugaba Erdogan ya ce: 'Gwamnatin Isra'ila na ci gaba da kawo cikas ga duk ƙoƙarin kawo ƙarshen yakin.'

'Idan akwai ko da ƙaramar dama ta sa makamai su yi shiru kuma a bude fili don tattaunawa, muna yin ƙoƙari na gaskiya don amfani da ita,' in ji shi.

'Fatanmu shi ne wannan yaki da ba ya kan ƙa’ida, mara ma'ana, wanda ba halastacce ba, kuma mai jawo asara ga bil'adama baki ɗaya ya zo ƙarshe cikin gaggawa.'

Erdogan ya kuma ce Turkiyya ta ƙara tsananta tuntuɓar diflomasiyya don ganin an sami tsagaita wuta.

Masu AlakaTRT Afrika - Isra’ila ce ummul aba'isin haramtaccen yaƙi da Iran: In ji Erdogan na Turkiyya

'Yayin da yaƙin ke ci gaba, mun yi gargaɗi cewa wuta na iya yaɗuwa zuwa wasu ƙasashe. Yayin da muke barin ranar 38 ta rikicin, abin takaici har yanzu muna ɗauke da irin waɗannan damuwa ga yankinmu,' in ji shi.

'A yayin da ake ci gaba da fuskantar haɗari, ni a matsayin shugaban ƙasa a gefe guda, da ministocinmu a ɗayan gefe, muna hanzarta tuntuɓarmu ta diflomasiyya,' ya kara da cewa.

Ya ce Isra'ila ta nuna cewa 'tana amfanar da kanta daga tashin hankalin' ta hanyar rufe Masallacin Ƙudus, da neman hukuncin kisa ga Falasɗinawa fursunoni, da ƙara tashin hankali a Lebanon da Siriya.

Erdogan ya ƙara jaddada cewa abubuwan da suka faru kwanan nan a yankin sun nuna muhimmancin tsarin 'Shirin Turkiyya marar ta'addanci' da aka ƙaddamar don ƙarfafa haɗin kai da zumunci a cikin ƙasa.

'A lokacin da ake yin ƙoƙarin gina katanga tsakanin Turkawa, Kurdawa, Larabawa, da Farisa, za mu iya kawar da waɗannan manaƙisa da shirinmu na Turkiyya marar ta'addanci da yanki marar ta'addanci,' in ji shi.

Rumbun Labarai
Yadda Turkiyya ke taimaka wa Iraƙi wajen isar da albarkatun manta zuwa kasuwannin ƙasa da ƙasa
An wallafa jawabin Shugaba Erdogan na UNGA-81 a matsayin littafi cikin harsuna uku
Shugaban Turkiyya Erdogan ya buƙaci haɗin ƙan Musulmai, ya soki nuna wariya
Emine Erdogan ta buƙaci a rabu da ‘al’adar jefar da kaya' a koma ga tsarin sabuntawa
Erdogan ya yi kira da a gyara MƊD, ya nemi a soke ikon kujerar na-ƙi
Abincin Afirka daga Turkiyya
Shugaba Erdogan na Turkiyya ya tafi New York taron Majalisar Dinkin Duniya
'Turkiyya za ta duba buƙatun Saudiyya ƙarƙashin yarjejeniyar Makkah yayin da Houthi ke kai hari'
An gano kwanson wani dodon koɗi mai shekara 66,000 a Ankara babban birnin Turkiyya
Turkiyya ta yi zarra a Shirin Ƙimar Dalibai na Duniya (PISA) 2025 a tsakanin ƙasashen OECD
Turkiyya ta yi Allah wadai kan girmama Ratko Mladic da aka yanke wa hukuncin laifin yaƙi
Turkiyya ba za ta bari a toshe hanyar ci-gabanta ba: Erdogan
Jiragen ruwa biyu na kasuwanci sun yi karo a gabar Tekun Silivri a Istanbul, mutum 10 sun ɓata
30 ga Agusta: Nasarar da ta buɗe hanyar tasowar Turkiyya ta zamani
An haƙo wani sassaƙen ɗan'adam zaune a kan damisa mai shekaru 11,000 a Turkiyya
Turkiyya ta ƙara haɓaka kasuwancin da take yi da ƙasashen Musulmi
Aselsan: Kamfanin tsaro na Turkiyya zai baje-kolin jirgin ƙarƙashin ruwansa a bikin Teknofest
Turkiyya ta ƙaddamar da shirin 2026–2030 na zama cibiyar fasahar AI ta duniya
Trump ya yi 'murna' kan yarjejeniyar tsaro ta Makka da Turkiyya da Pakistan da kuma Saudiyya suka yi
Shugaba Erdogan ya jinjina wa shekara 25 na Jam'iyyar AK kan samar da 'sauyi mai tarihi' a Turkiyya