| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Tirkashi: Real Madrid na so a ƙwace wa Barcelona kofuna 9, ta gabatar da ƙorafi mai shafi 50,000
Har zuwa yanzu, ofishin Mai Shigar da Ƙara yana kan bincike kan ko biyan kuɗaɗen na da niyyar yin tasiri kan hukuncin alƙalai, wanda ke nufin na cin hanci ne.
Tirkashi: Real Madrid na so a ƙwace wa Barcelona kofuna 9, ta gabatar da ƙorafi mai shafi 50,000
Ko a kakar bara ma Barcelona ce ta lashe kofin La Liga.

Ƙungiyar Real Madrid ta gabatar da wani rahoto mai shafi 50,000 ga hukumar ƙwallo ta Turai, UEFA, dangane da batun Negreira, wanda ake zargin Barcelona da bai wa alƙalan wasan La Liga cin hanci.

Madrid na neman a ƙwace wa Barca duka kofunan La Liga da ta lashe tsakanin 2001 zuwa 2018 lokacin da ake zargin laifukan sun faru, waɗannda suka kai har tara.

Batun Negreira wata taƙaddama ce da ta taso tsawon shekaru tun bayan binciken da aka yi a 2019 wanda ya gano cewa tsakanin 2001 da 2018, Barca ta biya kimanin euro miliyan 7.3 zuwa 8.4 ga kamfanonin da ke da alaƙa da Negreira, shugaban ƙungiyar alƙalan wasa.

Biyan kuɗaɗen ya dakata ne a 2018 lokacin da Negreira ya bar ƙungiyar alƙalan. Barcelona ta ce biyan kuɗaɗen halastacce ne da aka yi don biyan wasu ayyuka na ba da shawara, da samun bayanai kan alƙalan wasa don taimaka wa jami’an horar da wasa.

Dalilin zuwa gaban UEFA

Har zuwa yanzu, ofishin Mai Shigar da Ƙara yana kan bincike kan ko biyan kuɗaɗen na da niyyar yin tasiri kan hukuncin alƙalai, wanda ke nufin na cin hanci ne.

Da aka tambaye shi, Negreira ya gaya wa hukumomin haraji cewa Barcelona ta biya kuɗaɗen "saboda ka da a yi wani hukuncin da zai cutar da su", wato dai don samun garantin rashin tsoma baki.

A yanzu, Real Madrid ta kai Barcelona gaban mahukuntan UEFA game da kes ɗin, kuma ta bayyana cewa ta tura wani rahoto mai shafuka 50,000 ga UEFA.

A cewar shafin Real Madrid, "UEFA ta tabbatar da amsar ƙorafin da Real Madrid ta shigar kuma tana ci gaba da bincike kan biyan kuɗaɗen da Barcelona ta yi cikin shekaru 20 baya ga tsohon mataimakin Kwamitin Ƙwararru na Alƙalai."

A yanzu dai, rahotanni sun tabbatar da cewa Real Madrid ta zaɓi zuwa gaban UEFA ne saboda laifukan da ake zargin Barca, lokacin shari’a kansu ya wuce bisa dokar wasanni ta Sifaniya.