Meta, TikTok, YouTube na fuskantar tuhuma kan rashin kare yara, nacin amfani da manhajoji
Alkalan Kotun Los Angeles na iya kafa darasi ga dubban kararraki irin wannan tare da sauya fasalin yadda dokoki d ake kare kamfanonin fasaha za su yi aiki idan ana batun cutar da yara kanana.
Manyan kamfanonin fasaha uku a duniya na fuskantar shari'a mai muhimmanci a Los Angeles wadda za ta fara a wannan makon saboda ikirarin cewa shafukansu- Instagram na Meta, TikTok na ByteDance, da YouTube na Google - suna sanya naci da cutar da yara da gangan.
Zaɓen alkalai zai fara a wannan makon a Kotun Koli ta Gundumar Los Angeles. Wannan ne karo na farko da kamfanonin za su yi muhawara kan shari'arsu a gaban alkalai, kuma sakamakon zai iya yin tasiri sosai ga kasuwancinsu da kuma yadda za su tafiyar da yara ta amfani da manhajojinsu.
Ana sa ran tsarin zaɓen alkalan zai ɗauki aƙalla 'yan kwanaki, inda ake yi wa alkalai 75 tambayoyi kowace rana har zuwa nan da ranar Alhamis.
Kamfani na huɗu da aka ambata a cikin ƙarar, kamfanin Snapchat na Snap Inc., ya warware shari'ar a makon da ya gabata kan wani kuɗi da ba a bayyana nawa ba ne.
Ainihin dalilin shari'ar shi ne kan wata yarinya ‘yar shekara 19 da aka bayyana sunanta da harruffan "KGM," wadda shari'arta za ta iya tantance yadda dubban sauran ƙarar da aka yi shigar da kamfanonin kafofin sada zumunta za su gudana.
An zaɓe ta tare da wasu masu ƙara biyu don shari'ar da aka kai bellwether - musamman don gwada shari'o'i ga ɓangarorin biyu domin ganin yadda hujjojinsu za su kasance a gaban alkali da kuma irin diyyar da za a bayar idan ta kama, in ji Clay Calvert, wani babban jami'in nazarin manufofin fasaha a Cibiyar Harkokin Kasuwanci ta Amurka.
Fasalta zabi da manufar karfafa wa shigowar matasa
KGM ta yi iƙirarin cewa amfani da kafofin watsa labarunta tun tana ƙarama ya sa ta kamu maitar amfani da kayan na fasaha kuma hakan ya ƙara ta'azzara baƙin ciki da tunanin kashe kai.
Abin da ya fi muhimmanci shi ne, ƙarar ta yi iƙirarin cewa an yi hakan ne ta hanyar zaɓin ƙira da aka yi da gangan waɗanda kamfanoni suka yi waɗanda suka nemi su sa manhajojinsu su zama masu sanya jaraba ga yara don ƙara samun riba.
Wannan hujja, idan ta yi nasara, za ta iya kawar da bukatar Kwaskwarima ta Farko ta kamfanonin da Sashe na 230, wanda ke kare kamfanonin fasaha daga alhakin abubuwan da aka fitar da shafuka da manhajojinsu.
"Da suka ari irin salo da dabarun da injinan caca ke amfani da su wadand akamfanonini samar da sigari su ma suka dauka, waɗanda ake ƙarar sun saka wasu abubuwa na fasaha a cikin kayayakinsu da nufin haɓaka amfanin matasa don kara yawan kuɗin shiga na talla," in ji ƙarar.
Ana sa ran shugabannin zartarwa, ciki har da shugaban kamfanin Meta Mark Zuckerberg, za su ba da shaida a shari'ar, wadda za ta ɗauki makonni shida zuwa takwas.
Masana sun bayyana kamanceceniya da shari'o'in Big Tobacco wadda ta haifar da yarjejeniyar 1998 da ta buƙaci kamfanonin sigari su biya biliyoyin kuɗaɗen kiwon lafiya da kuma iyakance tallan da ke shafar ƙananan yara.
"Masu ƙara ba wai kawai lalatattun kayayyakin waɗanda ake ƙara ba ne," in ji ƙarar. "Su ne waɗanda suka illatu kai tsaye daga abubuwan da wadanda ake kara suka aikata da gangan Su ne waɗanda aka nufa don cim ma wasu manufofi masu cutarwa waɗanda suka ingiza su ga jerin martanin da za su iya lalata kansu da su."
Gwagwarmayar lafiyar kwakwalwa
Kamfanonin fasaha sun musanta ikirarin cewa kayayyakinsu suna cutar da yara da gangan, suna ambaton tarin kariya da suka ƙara tsawon shekaru kuma suna jayayyar cewa ba su da alhakin abubuwan da wasu kamfanoni suka wallafa a shafukansu.
"Kwanan nan, wasu ƙara sun yi ƙoƙarin ɗora alhakin matsalolin lafiyar kwakwalwa na matasa a kan kamfanonin sada zumunta," in ji Meta a cikin wani rubutu da aka yi kwanan nan a shafin yanar gizo.
"Amma wannan ya ƙara sauƙaƙa wata babbar matsala. Likitoci da masu bincike sun gano cewa lafiyar kwakwalwa matsala ce mai sarkakiya kuma mai fuskoki da yawa, kuma yanayin da ke tattare da lafiyar matasa ba a fayyace shi ko kuma ya zama ruwan dare gama gari ba.
Rage ƙalubalen da matasa ke fuskanta zuwa abu ɗaya ya yi watsi da binciken kimiyya da kuma matsalolin da ke shafar matasa a yau, kamar matsin lamba na ilimi, tsaron makaranta, ƙalubalen zamantakewa da tattalin arziki, da shan muggan kwayoyi."
Meta, YouTube, da TikTok ba su amsa buƙatun yin sharhi nan da nan ba a ranar Litinin.
Shari'ar za ta kasance ta farko a cikin shari'o'i da dama da suka fara a wannan shekarar da ke neman a dora alhakin lalacewar lafiyar kwakwalwa ga yara kanana.
Shari'ar da za a fara a watan Yuni a Oakland, California, za ta kasance ta farko da za ta wakilci gundumomin makarantu da suka kai kara kan shafukan sada zumunta kan cutar da yara kanana.
Bugu da kari, sama da lauyoyin jiha 40 sun shigar da kara a kan Meta, suna ikirarin cewa yana cutar da matasa kuma yana bayar da gudunmawa ga matsalar lafiyar kwakwalwa ta matasa ta hanyar tsara wasu siffofi a Instagram da Facebook da gangan wadanda ke sanya maita ga yara wajen amfani da shafukan.
Yawancin shari'o'in sun shigar da kararrakinsu a kotunan tarayya, amma wasu sun shigar da kara a jihohinsu.
TikTok ma na fuskantar irin wannan shari'ar a jihohi sama da goma sha biyu.