Morocco ta saki magoya bayan Senegal da aka ɗaure kan hargitsin wasan ƙarshe na AFCON

Mutane ukun sun bar gidan yari na Al Arjat 2, da ke arewa maso gabashin Rabat, a cikin motar ’yansanda don zuwa ofishin ’yansanda kafin daga bisani a sake su baki daya.

By
FILE PHOTO: CAF Africa Cup of Nations - Morocco 2025 - Final - Senegal v Morocco / Reuters

An saki magoya baya na kasar Senegal ne bayan sun kammala zaman gidan yari na tsawon watanni uku, inda aka mika su ga jami’an ofishin jakadancin Senegal.

A ranar Asabar ne kasar Morocco ta saki wasu magoya bayan Senegal su uku daga gidan yari bayan sun kammala zaman gidan yari na tsawon watanni uku saboda hannu a tashe-tashen hankula da suka barke a lokacin wasan karshe na cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) da aka gudanar a birnin Rabat.

Mutane ukun sun bar gidan yari na Al Arjat 2, da ke arewa maso gabashin Rabat, a cikin motar ’yansanda don zuwa ofishin ’yansanda kafin daga bisani a sake su baki daya.

Bayan barin ofishin ’yansandan, magoya bayan na Senegal su uku cikin murmushi sun samu tarbar mambobin ofishin jakadancin Senegal.

Daya daga cikinsu ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “dima Maroc, dima Maghrib” (wato “Allah Ya ja zamanin Morocco “).

Lauyan mai kare waɗanda ake zargin dan kasar Senegal, Patrick Kabou ya gode wa “wakilan diflomasiyya da na ofishin jakadancin kan kokarin da suka yi” a wani saƙo da ya wallafa a shafin  X.

A jajibirin sakin mutanen ukun, ya bukaci jama’a da su “ba su goyon baya, sannan sama da komai, su taimaka musu su saba da yanayin fita daga gidan yari.”

Wasu magoya bayan na ci gaba da kasancewa a garkame

Dangane da wannan shari’ar dai, wasu magoya bayan Senegal su 15 na ci gaba da kasancewa a garkame bayan sun samu hukuncin zaman gidan yari da ya tashi daga watanni shida zuwa shekara guda, hukuncin da kotun daukaka kara ta tabbatar a ranar Litinin.

An tsare su ne tun wasan karshe na ranar 18 ga watan Janairu—wanda Senegal ta yi nasara amma daga baya aka bai wa Morocco mai masaukin baki nasarar bayan daukaka kara—inda ake zarginsu da “tayar da tarzoma”, wanda ya hada da ayyukan tayar da hargitsi, musamman ga jami’an tsaro, da lalata kayayyakin wasanni, kutsa kai cikin fili, da kuma jifa da abubuwa.

Haka kuma, an saki wani dan kasar Faransa dan asalin Aljeriya a ranar Asabar bayan ya shafe watanni uku a gidan yari saboda jifa da kwalbar ruwa a lokacin wasan karshen.