Abin da zuwan kasuwar hannun-jarin Nijeriya ta farko a duniya ke nufi
NIJERIYA
3 minti karatu
Abin da zuwan kasuwar hannun-jarin Nijeriya ta farko a duniya ke nufiYaya abin yake a zahiri kuma me hakan yake nufi ga tattalin arzikin Nijeriya da kuma al’ummar kasar?
Kasuwar hannayen jari ta Nijeriya

Kasuwar hannun-jari ta Nijeriya ta zama ta farko a duk duniya wajen samun tagomashi a wannan shekara, cewar wani rahoto na mujallar tattalin arziki ta Bloomberg, wadda take bibiyar kasuwannin hannun-jari 92 a duniya.

Yaya abin yake a zahiri kuma me hakan yake nufi ga tattalin arzikin Nijeriya da kuma al’ummar kasar?

Abin da aka gano: Rahotan Bloomberg na makon jiya ya ce, bisa ƙididigar dalar Amurka kasuwar hannun-jari ta Nijeriya da a hukumance ake kira Nigerian Exchange Limited (NGX), ta zo kangaba wajen samar da riba, da daukakar darajar hannayen-jarin da ake hada-hadarsu, da kuma yawan cinikayyar da ake yi duk mako, idan aka yi la’akari da girman kasuwar.

Bloomberg ta ce daga farkon shekarar nan Nijeriya ce ta farko a kwazo, saboda ta samar da kashi 67% na riba a lissafin dalar Amurka, sai kuma Koriya ta Kudu mai biye mata da kashi 66%.

Abin da ya faru: Malam Ƙasimu Garba Kurfi, shugaban kamfanin hada-hadar hannayen-jari na APT Securities Limited a Nijeriya, ya ba da misali da hannun-jarin wani kamfanin siminti a kasuwar, wanda shekara biyu da ta wuce yake naira 32 ba, amma a yanzu ya kai naira 335.

Akwai kuma wani kamfanin inshora da aka hakikance shi ne ya fi kowanne ƙwazo, inda ya kawo ribar kusan kashi 1,400 a lissafin dala.

Dalilan faruwar hakan: Masana tattalin arziki sun ce wannan cigaba babbar alama ce da ke nuna yadda Nijeriya ke samun ƙaruwar ingancin manufofin tattalin arziƙin ƙasa, sakamakon sauye-sauyen haɓaka madafan tattalin arziƙi da gwamnatin ƙasar ke gudanarwa.

Sai ƙaruwar farashin ɗanyen mai a duniya, da haɓakar darajar naira a kasuwar musayar kuɗi, da kashi 4% kan dalar Amurka tun daga watan Janairu, wanda ya janyo masu zuba jari daga waje.

Yadda al’umma za ta ci gajiya: Malam Kasimu Kurfi ya ce, waɗanda suka zuba jari a wannan kasuwa ne suka fi damar more cigaban kasuwar ta hanyar karɓar ribar da kamfanonin da suka ci riba ke rabawa daga lokaci zuwa lokaci, ko kuma ta sayar da hannayen jarinsu bayan sun ƙara kima.

Akwai kuma wadanda suka mallaki kudade a wasu asusun da ake amfani da su wajen kasuwancin hannayen-jari.

Misali wanda ke ajiyar kudin fansho a kamfanin fansho da yake hada-hadar hannayen jarin kasuwar, to idan aka samu ribar hannun jari, kudin ajiyar fanshon nasa yana iya habaka.

Sai dai, Malam Kurfi ya ce zuba jari da kasuwancin hannayen-jari ta masu hakuri da jajircewa ce, ba masu neman arziki wuta-wuta ba.

Saboda akan iya daukar watanni ko shekaru kafin samun riba. Kafin sayen hannun-jari, ya wajaba mutum ya yi bincike ko ya nemi masana ko kamfanonin da aikinsu shi ne ba da shawara, ko kuma kamfanonin da suka iya juya dukiya an ba su amana.

Rumbun Labarai
WAEC ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 167,486
Dakarun Nijeriya sun kama mutanen da ake zargi da kai wa  'yan Boko Haram ƙwayoyi a Borno da Yobe
Gwamnati ta ba jami’o’i da kwalejojin Nijeriya umarnin korar ɗalibai da ke da alaka da satar mutane
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum 48 a samamen da suka kai maɓoyar masu laifi a Zamfara
An saki alƙalin da aka yi garkuwa da shi a jihar Kebbin Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun daƙile harin daren 'yanta'adda kan sansanin soji
'Yanbindiga sun kashe mutum 12, sun yi garkuwa da mata da yara a wani ƙauye Sokoto a Nijeriya
Nijeriya ta tura sojoji 86 domin aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau
Sojojin Nijeriya sun daƙile yunƙurin 'yanta'adda na garkuwa  da mutane 31 a Borno
Remi Tinubu ta nemi Saudiyya ta tallafa wa ilimin almajirai a Nijeriya
Nijeriya ta lalata makamai guda 2,819 da ta kama a matakin dakile rashin tsaro
'Yansandan InterPol sun tasa ƙeyar ɗan China daga Nijeriya kan safarar namun daji
Nijeriya na da attajirai 7,200 masu arzikin dala miliyan 1 duk da raguwar kuɗi - Rahoto
'Yanbindiga sun kashe Kanar na sojin Nijeriya bayan ya ƙi amincewa su yi garkuwa da shi
Aƙalla mutane 14 ne suka mutu a wani hari da aka kai a jihar Benue ta Nijeriya, in ji jami’an yankin
'Yanta'adda sun kashe aƙalla mutum 30 a wani ƙauye a Kaduna ta Nijeriya
Ana fargabar ɗalibai sun maƙale bayan da gini mai ɗakuna 90 ya rufta da su
Rundunar Sojin Nijeriya ta kama jami'in da ake zargi da sayar wa 'yanta'adda kayan soji
Jami'in da ke kula da harkokin kuɗin ISWAP ya miƙa wuya —Rundunar Sojin Nijeriya
INEC za ta rufe rijistar masu zaɓe ranar Lahadi, 'yan adawa na neman a tsawaita lokacin rijistar