Sojojin Nijeriya sun kashe 'yanta'adda da dama a Borno da Adamawa
Sojojin na Nijeriya sun samu nasarar ƙwato makamai da harsasai da bama-bamai daga hannun 'yanta'addan.
A wata gagarumar nasara a yaƙi da ta’addanci, sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa na Operation Hadin Kai sun kashe ’yanta’adda da dama a Jihohin Adamawa da Borno da ke arewa maso gabashing Nijeriya.
Mukaddashin Jami’in Watsa Labarai na rundunar, Laftanar Solomon Atokolo, ya ce nasarar ta biyo bayan dakile wasu hare-haren ’yanta’adda da aka shirya a sassa daban-daban na jihohin Arewa Maso Gabas.
Atokolo ya ce sojojin sun jawo wa ‘yanta’addan waɗanda ke tserewa asara babba a lokacin da suke kai musu farmaki.
“A safiyar ranar 16 ga Janairun 2026, ’yanta’adda sun yi yunkurin kwace sansanin sintiri a Sabon Gari da ke Karamar Hukumar Madagali a Jihar Adamawa, karkashin Sashe na 4 na OPHK. Sojojin da ke cikin shiri sun gaggauta tunkarar maharan, tare da samun tallafi daga dakarun da suka fito daga Gulak da kuma Rundunar Gaggawa ta Bataliya,” in ji shi a cikin wata sanarwa.
“An yi nasarar fatattakar ’yanta’addan ba tare da asarar rai ko kayan aiki daga bangaren sojojinmu ba, lamarin da ya tilasta musu barin harin,” in ji wani bangare na sanarwar.
A cewarsa, daga bisani an tsaftace yankin gaba ɗaya daga ‘yanta’adda tare da bincika shi domin gano nakiyoyi da tarko na bama-bamai, don tabbatar da tsaron fararen-hula da sojoji.
Haka kuma duk a rana ɗaya, ’yanta’adda sun kai wani babban hari daga fannoni da dama kan sansanin soji na FOB da ke Azir a Jihar Borno.
Maharan sun yi ƙoƙarin karya wani ɓangare na garkuwar tsaro, amma jaruman sojoji sun tarbe su inda suka buɗe musu wuta, tare da samun goyon bayan Sashen Sojojin Sama da sauran jiragen saman Rundunar Sojin Njeriya, lamarin da ya tilasta wa ’yanta’addan janyewa.
A yayin artabun, harbin makaman roka (RPG) da ’yanta’addan suka yi ya shafi motocin ɗaukar sojoji da ɗakin kula da kyamarorin CCTV, inda aka samu gobara a wani ɓangare, amma duk da haka sojojin sun ci gaba da rike cikakken iko da yanayin.
An kwato makamai da alburusai da dama daga hannun ’yanta’addan, ciki har bama-baman mortar da abubuwan fashewa da aka ƙera a gida, harsasan manyan bindigogi, da ɗaruruwan harsasan 7.62mm na NATO.