| hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Turkiyya, Masar, Qatar da Amurka sun sa hannu kan takardar yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza
An rattaba hannu kan wannan takarda ne a ranar Litinin yayin wani taron kasa da kasa da Masar ta shirya a wurin shakatawa na Bahar Maliya a Sharm el-Sheikh kan yarjejeniyar.
Turkiyya, Masar, Qatar da Amurka sun sa hannu kan takardar yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza
Turkiyya, Masar, Qatar da Amurka sun saka hannu kan yarjejeniyar Gaza
13 Oktoba 2025

Masar, Qatar da Turkiyya sun rattaba hannu tare da Shugaban Amurka Donald Trump kan wata takarda game da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

An rattaba hannu kan wannan takarda ne a ranar Litinin yayin wani taron kasa da kasa da Masar ta shirya a wurin shakatawa na Bahar Maliya a Sharm el-Sheikh kan yarjejeniyar.

Trump ya bayyana wannan rana a matsayin "babbar rana ga Gabas ta Tsakiya" yayin da shi da shugabannin yankin suka rattaba hannu kan wata sanarwa da aka tsara don tabbatar da tsagaita wuta a Gaza, bayan sa’o’i da Isra’ila da Hamas suka yi musayar fursunoni da wadanda aka yi garkuwa da su.

"Wannan babbar rana ce ga duniya, babbar rana ce ga Gabas ta Tsakiya," in ji Trump yayin da shugabannin duniya fiye da ashirin suka zauna don tattaunawa a taron.

"Takardar za ta fayyace dokoki da ka’idoji da sauran abubuwa da dama," in ji Trump kafin ya rattaba hannu, inda ya nanata sau biyu cewa "za ta tsaya daram."

Taron sake gina Gaza

Shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi ya bayyana cewa kasarsa za ta shirya wani taro kan sake gina Gaza bayan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni da wadanda aka yi garkuwa da su.

"Masar za ta yi aiki tare da Amurka da hadin gwiwar abokan huldar mu a cikin kwanaki masu zuwa don kafa tubali na sake gina Gaza, kuma muna shirin shirya taron farfado da tattalin arziki, sake gina da ci gaba," in ji shi.

Sisi ya kara da cewa yarjejeniyar Gaza "ta rufe wani babi mai radadi a tarihin dan Adam kuma ta bude wani sabon zamani na zaman lafiya da kwanciyar hankali" ga Gabas ta Tsakiya.

Ya kuma kara da cewa wannan rana ta zama "rana mai tarihi" ga zaman lafiya wadda ta shimfida hanya don warware matsalar kasashe biyu.

Rumbun Labarai
Israila ta rushe gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da sabon hari a Khan Younis
Trump ya ce “nan ba da jimawa ba” za a samar da dakarun tsaro na ƙasa da ƙasa a Gaza
Sau 27 Yahudawa 'yan-kama-wuri-zauna suka kutsa Masallacin Kudus a watan da ya wuce - Falasdinu
Bayanai na hukuma sun nuna cewa sojojin Isra'ila sun yi yunkurin kashe kansu sau 279 cikin wata 18
Hare-haren Isra'ila a Gaza sun kashe mutane 91, ciki har da yara 24, duk da tsagaita wuta
Netanyahu ya ba da umarnin a kai 'hare-hare masu karfi' kan Gaza
Shin Trump zai yanke alaka da Isra'ila idan ta ci gaba da mamaye Gabar Yammacin Kogin Jordan?
Amurka ta tsare ɗan jaridar Birtaniya Musulmi mai suna Sami Hamdi saboda sukar Isra'ila
Fiye da tan miliyan 61 na tarkace da baraguzai sun rufe Gaza a shekara biyu na yakin Isra'ila: UNRWA
Kalaman Trump na lalata cibiyoyin nukiliyar Iran 'mafarki ne': Khamenei
Wata ƙungiyar bayar da agaji ta Turkiyya ta ƙaddamar aikin kwashe ɓaraguzai a arewacin Gaza
Sojojin Israila sun buɗe wuta kan wasu manoma Falasɗinawa a yayin da suke girbe zaitun a Gaɓar Yamma
Mene ne abu na gaba a shirin zaman lafiya na Gaza?
Isra'ila ta sake buɗe mashigar Rafah don bai wa manyan motocin kayan agaji damar shiga Gaza
Dauwamammen zaman lafiya zai samu ne kawai ta hanyar kafa ƙasashe biyu, Erdogan ya faɗa wa Starmer
Sojojin Hamas sun kashe mutum 32 cikin 'gungun' da ke sace kayan agaji a Gaza
Hamas ta kammala sakin 'yan Isra'ila 20 da ta tsare a matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta
Wani bidiyo ya nuna yadda Isra'ila ke cin zarafin fursunonin Falasɗinawa gabanin sakin su
Trump, Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza a birnin Sharm el-Sheikh a ranar Litinin
Sojojin Amurka sun isa Isra'ila domin sa ido kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza