| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
4 minti karatu
Babban sojin Amurka na neman mafita daga yaƙin Iran yayin da damar soji ke daɗa raguwa: Rahoto
Janar Dan Caine ya yi wa masu bai wa Trump shawara hanunka-mai-sanda a ɓoye cewa ƙara faɗaɗa rikicin zai iya haddasa komabaya don mai yiwuwa ne hare-hare sama kaɗai ba za su iya cim ma abin da kasar ta sa a gaba ba, in ji rahoton kafar CNN ta Amurka.
Babban sojin Amurka na neman mafita daga yaƙin Iran yayin da damar soji ke daɗa raguwa: Rahoto
Shugaban manyan hafsoshin sojin Amurka Janar Dan Caine na bayani a wani taron manema labarai a Pentagon ranar 8 ga Afrilun 2026 a Arlington, Virginia.

Shugaban manyan hafsoshin sojin Amurka Janar Dan Caine ya yi kira a asirce ga manyan jami’an gwamnatin Trump su nemi wata hanyar rage yaƙin Amurka da Iran, cikin damuwa cewa zaɓi na soji da ƙasar ke da su za su iya samar da ƙayyadadden sakamako ne kawai tare da haddasa ramuwar gayya mai yawa, in ji rahoton.

Da take ambatar majiyoyi uku da ke da masaniya game da tattaunawar, kafar watsa labaran CNN ta Amurka ta ba da rahoton cewa Caine ya nuna damuwarsa ga manyan jami’an gwammnatin ciki har da daraktan hukumar leƙen asiri ta CIA John Ratcliffe, da sakataren harkokin waje Marco Rubio da Mataimakin Shugaban Ƙasa JD Vance.

Rahoton ya ce Caine da sauran jami’ai sun yi ammanar cewa da wuya ƙarfin sojin sama kawai ya tilasta wa Tehran ta yarda da buƙatun Amurka, duk da cewa Shugaba Donald Trump ya ci gaba da nuna fifiko ga kauce wa tura dakaru ta ƙasa.

Kazalika ya ce Caine da sauran manyan jami’ai sun yi shakkar aikin shawarar ƙara faɗaɗa yaƙin a ƙarshen watan Yuli, saboda damuwa game da ramuwar gayya ta Iran kan ƙawayen Amurka da kuma kayayyakin makamashi na yanki. Sai dai Trump ya ɗaga hare-haren bayan da ƙawaye na yankin Gulf suka yi gargaɗin yiwuwar samun hare-haren ramuwar gayya, in ji rahoton.

Ya kuma bayyana ƙarin damuwa game da ƙarewar tarin makaman Amurka ciki har da makaman tsaron sararin samaniya na kakkaɓo makamai da sauran makamai masu seti da za su iya taƙaita ikon Washington na daɗewa a yaƙi.

Da take bayyana cewa Caine ya yi gargaɗi ga Trump game da haɗura na soji, CNN ta ce ya kuma jaddada cewa sojin Amurka za su iya lalata abubuwa da yawa a Iran idan aka ba su umarnin faɗaɗa yaƙin.

Rahoton ya ce jami’an gwamnatin suna neman wani sakamako da Trump zai iya bayyanawa a matsayin nasara ta siyasa yayin da yake barin ƙofar diflomasiyya a buɗe, ciki har da yiwuwar yarjejeniyar sake buɗe Mashigar Hormuz.

Yaƙin Amurka da Iran

Tashe-tashen hankula na yanki sun faɗaɗa ranar 28 ga watan Fabrariru a lokacin da Isra’ila da Amurka suka ƙaddamar da yaƙi tare kan Iran inda suka mayar da hankali kan wuraren soji da da nukiliya da makamashi da ababen morea rayuwa na fararen hula, inda hare-hare suka kashe Jagoran Addinin Ƙasar da ya daɗe, Ali Khamenei, da kuma da yawa daga cikin manyan jami’an gwamnatin ƙasar, tare da ɗaruruwan fararen hula.

Amma Iran ta mayar da martani cikin gaggawa ta hanyar karɓe iko da Mashigar Hormuz, tsukakkiyar hanyar inda kashi ɗaya cikin biyar na man duniya ke wucewa a jiragen ruwa, kuma ta yi ruwan makamai masu linzami da jirage mara matuƙa kan ƙasashen yankin Gulf.

Masu AlakaTRT Afrika - Trump ya dakatar da kai wa Iran hari saboda karancin makaman tsaron samaniya — rahoto

A ranar 18 ga watan Yuli, Iran da Amurka sun rattaɓa hannu kan wata takardar fahimtar juna ta hanyar shiga tsakanin Pakistani da Qatar, lamarin da ya kawo ƙarshen hare-hare kai tsaye da kuma ƙaddamar da tattaunawa domin samun yarjejeniya ta ƙarshe.

Tattaunawar ta kuma katse kan ce-ce-ku-ce bisa tsaron tafiya a kan ruwa da kuma ‘yancin tafiya a ruwa ta Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar fitar da mai da gas daga yankin Gulf.​​​​​​​

Wani jami’in Amurka ya bayyana ranar Jumma’a cewa an samu ci-gaba tsakanin Iran da Oman da zai iya sake buɗe Mashigar Hormuz, lamarin da zai iya sake dawowa da fitar da mai da yaƙin Amurka kan Iran ya katse.

Jami’in na Amurka, wanda ya ƙi a bayyana ko shi wane ne, ya ce Washington na ganin za a cim ma yajrjejeniya nan ba da jimawa ba tsakanin ƙasashen biyu, da ke ko wane gefe ɗaya na mashigar, domin kaikomo ya sake dawowa.

Wata yarjejeniya tsakanin Iran da Oman game da iko a kan muhimmiyra hanyar ruwan ana ganin wata muhimmiyar yarjejeniya ce cikin yarjejeniyar zaman lafiya.

"Akwai ci-gaba tsakamin Oman da Iran a kan mashigrar, kuma muna tsammanin wata yarjejeniya nan ba da jimawa ba," kamar yadda wani jami’in Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labran Reuters ranar Jumma’a.


Rumbun Labarai
Amurka na yaƙar Iran ne don kare ƙawayenta a Gabas ta Tsakiya da ƙasashen Yamma - Trump
Iran ta ce harin bam na Amurka a wajen bikin aure a Hormozgan ya kashe fararen hula
Kakakin Majalisar Dokokin Iran ya buƙaci ’yan kasa su rage amfani da fetur
Iran ta ce ta kai hari sansanin sojin Amurka da ke UAE, ta harbo jiragen leken asiri na ƙasar
Harin Amurka a Tsibirin Larak na Iran ya kashe mutane da dama da kuma jikkata wasu
Karshen ayyukan 'yan ta'addar PKK/YPG
Yarjejeniyar Makka na aike wa da 'Saƙon haɗin kai da zaman lafiya': Firaministan Pakistan
Shugaban Siriya ya naɗa tsohon shugaban ƙungiyar SDF/YPG a matsayin mai ba shi shawara
Babbar ɗimuwar Netanyahu: Mafarkin Turkiyya na shirin kai hari
Shugaban Iran ya yi kira ga ƙasashen Musulmai su daina bari ana kai hare-hare daga cikin ƙasashensu
Hare-haren Iran sun ragargaza cibiyoyin leken asirin Amurka a Gabas ta Tsakiya: Rahoto
Iran ta yi gargaɗin cewa yaƙi da Amurka nan gaba zai iya shafar duka shiyyar da ma fannin makamashi
Trump ya ce an cire abubuwan fashewa daga Mashigar Hormuz, ya gargaɗi Iran kan dasa wasu
Saudiyya da Faransa sun goyi bayan kafa ƙasar Falasɗinu, sun buƙaci Isra’ila ta janye daga Lebanon
Hantarar da Amurka ke yi mana za ta ta'azzara ƙoƙarin diflomasiyya, in ji Iran
Iran ta ci gaba da nuna rashin tsoro yayin da Amurka ke ci gaba da ƙara mata matsin lamba
Ya kamata yaƙi da Amurka ya ƙare yayin da Tehran ke da  'iko da mutunci': Pezeshkian
Sabbin takunkuman da Amurka ta saka mana ta'addanci ne a fannin tattalin arziki, in ji Iran
Tsohon Ministan Tsaron Isra'ila Yaalon ya zargi Netanyahu da neman rikici da Turkiyya
Ko dabarun yaƙi na Iran za su sanya Amurka sake tunani?