An kashe ‘yanta’addan ISWAP fiye da 40, ciki har da wani babban kwamanda, a wasu jerin hare-haren sama da dakarun sojin Nijeriya suka kai a maɓoyarsu a ƙaramar hukumar Guzamala ta jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar a ƙarshen mako, kamar yadda wata sanarwar sojin ƙasar ta bayyana.
Sanarwar da jami’in watsa labaran soji na hedkwatar runduna ta musamman ta Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni ya fitar a Maiduguri ranar Litinin, ta bayyana cewa nasarar ta samu ne bayan an samu bayanan sirri masu tushe na taruwar ‘yanta’addan ISWAP a ƙauyen Badu, kudu da Gudumbali da ke ƙoƙarin ƙaddamar da hare-hare kan dakarun sojin a inda suke aiki.
“Yayin da yake aiki cikin gaggawa bisa bayanan sirri, ɓangaren sojin sama [na rundunar Operation Haɗin Kai] ya tattara bayanan sirri ta sama da kuma gano tafiyar ‘yanta’adda kusa da wuraren da ake zargin maɓoyarsu ce, inda sojoji suka ƙaddamar da hari kai-tsaye kan wani ginin da ‘yanta’adda suke ciki”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Bayanan farko sun nuna cewa fiye da ‘yanta’adda 40, ciki har da wani babban Qaid na ISWAP (kwamanda), ne suka mutu a harin.
“Samamen ya kuma lalata motoci biyu da kimanin babura 20 da ‘yanta’addan ke amfani da su domin tafiya da sarrafa abubuwa da kuma kai samame, lamarin da ya kassara ikonsu na yaƙi da kuma daƙila hare-haren da suka shirya kaiwa kan wuraren sojoji da kuma al’ummomin da ke yankin,” in ji rundunar.
“Ƙarin bayanan sirri sun nuna cewa ‘yanta’addan sun fito ne daga ISWAP ɓangaren Murabitun, wani ɓangaren yaƙi na musamman da ke sintiri da kuma jagorantar hare-hare da yin ta’addanci a yankin,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Lalata maɓoyar da kuma kayayyakin masu alaƙa da sarrafa abubuwan wata alama ce ta babban koma-baya ga ikon ƙungiyar na ƙaddamar da hare-hare a yankin Tafkin Chadi.”
Rundunar sojin ta bayyana cewa ana ci gaba da tattara bayanai daga wurin domin tabbatar da girman ɓarnar da samamen ya yi wa ‘yanta’addan.
“Samamen da aka yi nasarar kaiwa ya nuna ingancin hare-haren saman da ake yi bisa bayannan sirri da fasaha wajen tarwatsa ƙungiyoyin ‘yanta’adda da tarwatsa aika-aikar abokan gaba da kuma hana masu aikata laifuka ‘yancin aika-aika,” in ji sojin.
“Ya kuma nuna yadda dakarun Operation HADIN KAI ke ci gaba da aikin kassara ‘yanta’adda da kuma ƙarfafa tsaro a faɗin Arewa Maso Gabashin [Nijeriya]”, in ji sanarwar.
Rundunar haɗin gwiwar ta Arewa Maso Gabashin Nijeriya ta ce ta jajirce wajen wargaza barazanar ‘yanta’adda da kare al’ummomi masu rauni da kuma ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi wajen sake dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.





















