| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Ministan Tsaron Isra'ila ya ce rusa Gaza yana sa shi 'nishaɗi'
Ministan tsaron Isra'ila Israel Katz ya ce yana jin daɗin yadda ake lalata yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda ya ba da shawarar kafa matsugunan Yahudawa na dindindin a arewacin Gaza.
Ministan Tsaron Isra'ila ya ce rusa Gaza yana sa shi 'nishaɗi'
Katz ya ce tuntuni yake da niyyar kafa sansanonin Nahal guda uku a wuraren da suke arewacin Gaza kafin ficewar Isra'ila daga yankin a shekarar 2005.

Ministan tsaron Isra'ila Israel Katz ya ce barnar da aka yi a yankin Gaza da aka killace tana sa shi "nishaɗi," yana mai bayyana hakan a matsayin sakamakon abin da ya kira "manufar da aka yi da gangan" da nufin kawar da duk wata barazana.

A jawabinsa a yayin rangadinsa a yankin arewacin Gaza, wanda tashar talabijin ta 14 ta Isra'ila ta yaɗa a ranar Litinin, Katz ya kuma sanar da shirin kafa wasu matsugunai uku da ke da alaƙa da sojoji a yankin.

Yayin da aka tambaye shi game da yadda yake kallon barnar da aka yi a Gaza, Katz ya amsa da cewa: "yanayi mai ƙyau, ko ba haka ba?" Ya yi iƙirarin cewa barnar ta samo asali ne daga "manufar da aka yi da gangan" wadda aka tsara don kawar da duk wata barazana.

Ya ce Isra'ila ta yi watsi da dabarunta na baya na kai hare-hare na ɗan lokaci, sannan ya ƙara da cewa: "Maimakon shiga da fita, yanzu sojoji suna ciki, 'yanta'adda kuma suna waje, sannan ana rusa gidaje ."

Matsugunin Yahudawa na dinɗinɗin a Gaza

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka ɗau hankali a rangaɗin Katz shi ne buƙatarsa ta kafa matsugunan dindindin na Yahudawa a arewacin Gaza, a cewar kafar Channel 14.

Katz ya ce tuntuni yake da niyyar kafa matsugunan Nahal uku a wuraren da ake da su a arewacin Gaza kafin ficewar Isra'ila daga yankin a shekarar 2005.

Sansanonin Nahal wurare ne da ke da alaƙa da matsugunan sojoji waɗanda a baya ake amfani da su don kafa sabbin matsugunan kafin su zama al'ummomin farar hula.

Katz ya yi iƙirarin cewa matakin ya zama dole saboda dalilai na "tsaro", yana mai cewa zai ƙarfafa ikon Isra'ila da "kare" al'ummomin da ke kusa idan lokaci ya yi.

Isra'ila ta kashe Falasdinawa fiye da 73,000, waɗanda galibi mata da yara ne, tare da jikkata fiye da 173,000 a yakin kisan kare-dangin da ta yi a yankin da aka killace tun daga watan Oktoban 2023.

Kazalika ta mayar da mafi yawan yankin zuwa kango tare da korar al'ummar yankin baki ɗaya.