| Hausa
SIYASA
4 minti karatu
Hillary Clinton ta nemi Amurka ta ɗauki mataki mai tsauri idan Isra'ilawa suka sake zaɓen Netanyahu
"Na sha faɗa cewa, ina son Isra'ila amma na tsani gwamnatin Netanyahu da manufofinsa," a cewar Tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton kan zaɓen ƙasar da ke tafe a watan Oktoba mai zuwa.
Hillary Clinton ta nemi Amurka ta ɗauki mataki mai tsauri idan Isra'ilawa suka sake zaɓen Netanyahu
Hillary Clinton ta yi kira ga Amurka da ta dauki mataki mai tsauri idan 'yan Isra'ila suka sake zaben Netanyahu

Tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta yi kira ga Amurka da ta ɗauki mataki mai tsauri idan Isra'ilawa suka sake zaɓen gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu wadda ta samu goyon bayan Jam'iyyar Democrat sosai a yayin kisan ƙare-dangi da ta yi wa Falasɗinawa a Gaza.

"Don haka idan Isra'ilawa suna son sake zaɓen wannan gwamnati, to ina ganin ya kamata Amurka ta ɗauki mataki mai tsauri," in ji Clinton yayin wata zantawa da ta yi da kafar watsa labarai ta MS Now game kan babban zaɓen Isra'ila na ranar 27 ga watan Oktoba da ke tafe.

Clinton ta yi nuni kan wasu rahotanni da ke cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta gargaɗi Netanyahu kafin ranar 7 ga Oktoban 2023, game da shirye-shiryen ƙungiyar Hamas na kai kaiwa Isra'ila hari.

Wataƙila Netanyahu bai yarda da gargaɗin ba ne ko kuma ya yi tunanin yadda zai yi amfani da lamarin don cim ma manufarsa ta ɗaukar "mataki mai tsauri," wanda hakan "zai ƙarfafa matsayinsa," in ji ta.

"Wannan gazawa ce ta shugabanci, sannan gazawa ce ta kare al'ummar Isra'ila," in ji Clinton game da Netanyahu, wanda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ke nema ruwa-a-jallo kan zargin aikata "laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil'adama a Gaza."

"Na sha faɗa cewa, ina son Isra'ila amma na tsani gwamnatin Netanyahu da manufofinsa," in ji ta.

"Ina son Amurka amma na tsani gwamnatin Trump da manufofinsa," in ji ta a yayin da take magana game da Shugaba Donald Trump, wanda ya ƙalubalance ta a zaɓen 2016 da ta sha kaye, lamarin da ya bai wa Trump damar fara wa'adinsa na farko a kan karagar mulki.

Haka kuma, Clinton ba ta yi tsokaci game da tsohon Shugaba Joe Biden da kuma babbar rawar da jam'iyyarta ta Democrat ta taka wajen bai wa Isra'ila damar ci gaba da kisan ƙare-dangi a Gaza ta hanyar samar da makamai masu yawa da kuma goyon bayan diflomasiyya.

Kungiyoyin kare hakkin ɗan’adam da masu suka na ganin cewa wannan goyon bayan ne ya sa gwamnatin Amurka a ƙarƙashin mulkin Biden ta zama mai hannu wajen kisan gillar da aka yi wa Falasɗinawa da kuma rikicin jinƙai a Gaza.

Rikicin ‘yan kama-wuri-zauna na Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan

Clinton ta ce za a samu gagarumin sauyi idan Netanyahu ya sauka daga kan mulki a matsayin Firaminista: "Ina kuma fatan sabon Firaminista zai ɗauki mataki mai tsauri kan tashe-tashen hankulan da ‘yan kama-wuri-zauna na Isra’ila ke haddasawa a Yammacin Kogin Jordan.

Bai kamata a bar masu aikata irin wannan tashin hankali su tsere ba tare da sun fuskanci hukunci ba." Ta yi gargadin cewa barin mutane su samu irin wannan dama a cikin al'umma "ba daidai ba ne kuma ba a kyautata wa "Falasɗinawa ba” kuma "yana da matuƙar hatsari" ga Isra'ila.

"Duk lokacin da ka bar mutane suna aikata irin wannan mummunan tashin hankali a cikin al'umma, kuma ba ka hana ba, zai gurgunta al'umma baki ɗaya," in ji Clinton.

Kalaman Clinton sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun hare-haren sojoji da na ‘yan kama-wuri-zauna na Isra'ila a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye tun farkon soma kisan ƙare-dangi a Gaza a watan Oktoban 2023.

Hukumomin Falasinawa sun tattara bayanan kisan gilla da sace-sace da rushe-rushen gidaje da hare-hare kan masallatai da ababen hawa da kuma lalata gonaki da sanya takunkumi kan damar manoma su shiga gonakinsu da kuma tilasta musu yin hijira.

Falasɗinawa sun yi gargaɗin cewa kisan gillar da Isra'ila ta yi wa mazauna yankin na share fagen mamaye Yammacin Kogin Jordan, wanda kuma hakan zai kawo cikas ga kafa ƙasar Falasɗinu a ƙarƙashin ƙudurorin Majalisar Dinkin Duniya.