Tawagar Super Falcons ta Nijeriya za ta kara da tawagar Indomitable Lionesses ta Kamaru ranar Lahadi a wasan kwata-fainal da tawagogin za su yi a Gasar kofin Afirka da ake yi a Maroko.
Fafatawar da za su yi a filin wasa na Larbi Zaouli da ke Casablanca, ba kawai za ta samar da mai zuwa matakin daf da na ƙarshe na gasar WAFCON ɗin ba ne tsakanin tawagogin biyu, shi zai bai wa ɗaya daga cikin tawagogin biyu damar zuwa Gasar Kofin Duniya ta mata kai-tsaye.
Ƙasashe biyun dai sun kai ga matakin sili-ɗaya-ƙwale ne daga rukuni daban daban.
Saɓanin yadda aka saba gani, tawagar koci Justine Madugu ta Nijeriya ta kai ga wasa na ƙarshe na matakin rukuni-rukuni ne a ƙarƙashin matsi mai yawa sakamakon kayen da ta sha a hannun Malawi da ta fara shiga gasar a bana da ci 2-3.
Sai dai kuma tawagar ta samu ta farfaɗo inda suka samu ta yi nasara kan tawagar Zambia da ƙyar.
Duk da cewa tawagar ta samu gagarumar nasara da ci 2-6 kan tawagar Cleopatras ta Masar, babbar tawagar ta nahiyar Afirka ta samu ta shiga mataki na biyu ne kawai a rukunin C a bayan Malawi, wadda ta sha kaye a hannun Zambia a ranar ƙarshe ta wasannin rukunin.
Nasarar ta bai wa tawagar da ta lashe gasar WAFCON sau 10 damar kece reni da abokan hamayya daga Kamaru a wani wasa da zai sake fito da hamayyar wasan ƙwallon ƙafa tsakanin tawagogin ƙasashen biyu.
Kamaru saɓanin abokiyar hamayyarta, ba ta sha kaye ba a wanna gasa ta bana. Tawagar Indomitable Lionesses ta doke Mali da Ghana a wasanninta biyu na farko.
Bayan ta riga ta samu tabbacin kasancewa tawaga ta farko a rukuninta ta D, tawagar ta tashi canjaras da tawagar ƙwallon ƙafa ta Cabo Verde inda ta gama wasanninta na rukuni-rukuni da maki bakwai.
A lokacin ɓangarorin biyu suka fito fili ranar Lahadi, abin da za su fi mayar da hankali a kai ba kawai alfahari ba ne. Tawagar da ta yi nasara a wasan za ta samu shiga Gasar Kofin Dunita ta Mata ta 2027 kai-tsaye tare da sake matsawa kusa da lashe Gasar kofin Afirka ta Mata.
Ga Kamaru, nasara a kan tawagar da ta fi nasara a tarihin Gasar Kofin mata ta Afirka za ta ƙara mata suna ne yayain da take ƙoƙarin sake nuna ƙarfinta a fagen tamaula a nahiyar bayan ta gaza shiga gasar WAFCON da ta gabata.
Bayan ta lashe gasar sau 10, tawagar Super Falcons –duk da kayen da ta sha da farkon gasar ta bana– tana son tabbatar da matsayinta na tawagar da ta fi nasara a ƙwallon ƙafar mata a nahiyar Afirka.
Tawagar Super Falcons ta fi tawagar Kamaru damar iya nasara idan za a yi la’akari da tarihin gasar WAFCON. Yayin da tawagogin biyu suka fafata sau 13 a tarihi, Nijeriya ta doke Kamaru sau 9 a wasannin da suka ƙare cikin lokacin wasa yayin da Kamaru ta doke Nijeriya sau ɗaya. An tashi a ɗaya daga cikin wasannin ne canjaras.
A karawarsu ta ƙarshe, a gasar WAFCON ta shekarar 2022, Nijeriya ta samu ta kai matakin daf da na ƙarshe bayan da ta doke Kamaru da ci ɗaya da nema.
Tsakanin Kamaru da Nijeriya wace tawaga za ta samu tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta Mata?
Yayin da za a fara wasan kwata-fainal na ranar Lahadi tsakanin Nijeriya da Kamaru, tawagogin biyu za su kasance suna da abubuwa da suke son cim ma.
Ga tawagar Super Falcons, wata dama ce ta faɗaɗa nasararta a nahiyar, yayin da Indomitable Lionesses za ta nemi ta koma sahun gaba-gaba a manyan tawagogin Afirka.





















