Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi maraba da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka ayyana ta kawo ƙarshen rikicin Amurka da Iran, yana mai bayyana shi a matsayin wani muhimmin ci-gaba ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
"Ina ganin yarjejeniyar da aka cim ma tsakanin Amurka da Iran a matsayin wani muhimmin ci-gaba na rinjayen zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, kuma na yi maraba da shi da jindaɗi," kamar yadda Shugaba Erdogan bayyana .
Ya nuna fatansa na gaskiya cewa wannan labarin, wanda duniya gabaɗaya ta daɗe tana buƙata, zai janyo wani yanayi mai ɗorewa na zaman lafiya da tsaro.
Shugaba Erdogan ya kuma jaddada buƙatar kauce wa kamalai da ayyuka na taɓarɓarewa lamura da tsokana a cikin lokacin da ya saura kafin bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar, yana mai jaddada cewa dole dukkan ɓangarorin su yi taka-tsan-tsan kan yiwuwar zagon ƙasa.
"Na gode wa Pakistan game da namijin ƙoƙarinta na shiga-tsakani, tare da shugabannin Amurka da Iran, wajen cim ma wannan sakamakon.
“Ina kuma so na bayyana godiyata ga goyon bayan da Qatar da Saudiyya suka bayar ga waɗannan shirye-shiryen diflomasiyya," a cewarsa, yana mai jaddada cewa Turkiyya za ta ci-gaba da goyon bayan dukkan wani ƙoƙari na samar da mafita mai ɗorewa bisa diflomasiyya da dokokin ƙasa da ƙasa.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Ministan Harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce Turkiyya tana yi wa yarjejeniyar kyakyyawan kallo kuma ya bayyana fatan cewa za a ci gaba da tattaunawa a cikin wani yanayi na neman maslaha.
"Muna maraba da da yarjejeniyar da aka cim ma da zummar kawo ƙarshen yaƙi tsakanin Amurka da Iran," kamar yadda Fidan ya bayyana.
Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin "wani muhimmin ci-gaba wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a yankin".
Ita ma Qatar ta yi maraba da yarjejeniyar da aka cim ma a wata takardar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran ta warware matsaloli tsakaninsu, ciki har da tabbatar da ‘yancin wucewa ta Mashigar Ruwan Hormuz, da kuma yi masa kallon muhimmin mataki zuwa tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma inganta ci-gaban tattalin arziki a yankin da ma duniya bakiɗaya.
Turai ta yi kira ga gaggauta aiwatar da yarjejeniyar
Shugabannin Faransa da Birtaniya da Jamus da kuma Italiya sun nuna goyon baya ga sabuwar takardar fahimtar juna da aka ayyana tsakanin Amurka da Iran, suna masu mai kiranta wata nasara ta diflomasiyya tare da kira da a gaggauta aiwatar da ita.
A wata sanarwa, shugabannin ƙasashe huɗun sun taya Amurka da Iran murna har ma da masu shiga tsakani da ke da hannu a yarjejeniyar, ciki har da Pakistan da Qatar.
Da yake maraba da yarjejeniyar, shugaban gwamnatin Jamus ya bayyana ta a matsayin wata muhimmiyyar ci-gaba da zai buɗe hanyar samar da Gabas Ta Tsakiya mai ingancin tsaro da kuma tattalin arziki mai ƙarfi.
Firaministan Japan ta yi maraba da yarjejeniyar Amurka da Iran domin kawo ƙarshen rikici da fatan cewa za a aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, ciki har da sake buɗe Mashigar Ruwan Hormuz domin wucewar jiragen ruwa ƙasa da ƙasa, kamar yadda Firaminista Sanae Takaichi ta bayyana ranar Litinin.
Da yake shiga cikin jerin ƙasashe duniya da ke goyon bayan lamarin, sakataren janar na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) Antonio Guterres ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani mataki mai kyau.
"Ina taya Amurka da Iran murna domin sun cim ma yarjejeniyar zaman lafiyar ta samar da tsagaita wuta na din-din-din nan-take da sake buɗe mashigar ruwan Hormuz tare da tsarin ƙarin tattaunawa," in ji Guterres .
"Wannan wani muhimmin mataki ne zuwa warware rikicin ."
“‘Yancin wucewar jirage ba tare da tsaiko ba”
Sanarwar ta Turai ta yi kira da a sake buɗe mashigar ruwan Hormuz cikin gaggawa da "‘yancin wucewar jirage mara tsaiko da sharaɗi," tana mai bayyana matakin a matsayin abu mai muhimmanci.
Ƙasashen huɗun sun ce sun shirya wajen ba da gudumawa ga cim ma wannan manufa, ciki har da ta hanyar "wata tawaga ta tsaro kawai mai cin gashin kanta " da zummar tabbatar da wucewar jiragen ruwan na jigilar kayayyakin kasuwa da kuma aiwatar da ayyukan kawar da nakiya.
Shugabannin sun nuna yardarsu da sauƙaƙa takunkumai da masu alaƙa idan Iran ta ɗauki "matakai bayyanannu da za a iya tabbatarwa" bisa shirin nukiliyarta .
Sun kuma sake tabbatar da goyon bayansu ga zaman lafiya da ‘yancin kai da mutunta ‘yancin kan iyakan Lebanon, suna masu jaddada muhimmancin tabbatar da wani "tsagaita wuta mai ƙarfi."







.jpeg?width=512&format=webp&quality=80)






