| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kashe matarsa da fatanya a Kebbi
Jami’an ’yan sanda a Jihar Kebbi sun kama wani mutum mai shekara 30, mai suna Suleman Mamuda, bisa zargin kashe matarsa, Umaima Maidawa, a garin Bayawa da ke Karamar Hukumar Augie ta jihar.
'Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kashe matarsa da fatanya a Kebbi
'Yansandan Nijeriya / Others
16 Janairu 2026

Jami’an ’yan sanda a Jihar Kebbi sun kama wani mutum mai shekara 30, mai suna Suleman Mamuda, bisa zargin kashe matarsa, Umaima Maidawa, a garin Bayawa da ke Karamar Hukumar Augie ta jihar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce ana zargin wanda ake tuhuma da buga wa matarsa da fartanya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.

A cewarsa, Mamuda ya tsere daga yankin bayan faruwar lamarin, amma daga bisani ’yan sanda sun gano inda yake tare da kama shi bayan gudanar da bincike da kuma samun sahihan bayanai daga al’ummar yankin.

 “Ya tsere daga yankin bayan faruwar lamarin, amma an gano inda yake tare da kama shi sakamakon binciken ’yan sanda da bayanan da aka samu daga al’ummar yankin,” in ji shi.

SP Usman ya ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Umar Mohammed Hadejia, ya bayar da umarnin mika shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da bincike da kuma gurfanar da wanda ake tuhuma.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani lamari cikin gaggawa tare da ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.

 

 

Rumbun Labarai
Jan hankalin gwamnatin Nijeriya ga 'yan ƙasar masu shiga yaƙi a wasu ƙasashen ƙetare
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta daƙile hare-haren 'yan ta'adda a jihar Borno
Nijeriya ta gargaɗi ‘yan ƙasar kan faɗawa tarkon masu ɗaukar ma’aikata su tura su wurin yaƙi
'Yanbindiga sun kashe aƙalla mutum 30 a Jihar Neja ta Nijeriya, sun ƙona ofishin 'yansanda
'Yanbindiga sun kashe DPO na 'yansandan Nijeriya a Jihar Katsina
'Rashin sake wa hukumomin gwamnatin Nijeriya kuɗaɗen kasafi koma-baya ne ga ci gaban ƙasa'
Za a yi zaben Shugaban Kasa a Nijeriya ranar 20 ga Fabrairun 2027, in ji INEC
Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Nijeriya ta kori ma'aikatanta 43 kan saɓa wa dokar aiki
Jami'an tsaro sun ƙwace fasfon Nasir El-Rufa'i bayan yunkurin kama shi ya ci tura a filin jirgi
Sojojin Nijeriya sun kashe 'yan Boko Haram 16 a Borno
CBN ya bai wa 'yan canji a Nijeriya damar sayen dala 150,000 a duk mako daga gwamnati
Amurka za ta tura sojojinta 200 Nijeriya
Sojojin Nijeriya sun kashe gomman 'yan-ta'adda, sun dawo da mutum 700 gida a arewa maso gabas
Me ya sa Kannywood ke fafutuka yayin da Nollywood ke samun tagomashi?
Shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan ya ajiye aikinsa
Mutum fiye da 30 sun rasu sakamakon hatsarin mota a Jihar Kano
Nijeriya: 'Yanbindiga sun sace wani faston Katolika a Kaduna, sun kashe mutum uku
Nijeriya da Nijar sun ƙulla yarjejeniya kan jigilar kayayyaki da tsaron kan iyaka
Shugaba Tinubu na Nijeriya na shirin kai ziyarar aiki London a watan Maris
Jerin hare-hare sun yi sanadin mutuwar mutum 30 a Jihar Benue ta Nijeriya