Kiristoci Falasɗinawa sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a Gaza da Gaɓar Yamma
Falasɗinawa mabiya addinin Kirista sun gudanar da bikin Kirsimeti a karon farko tun 7 ga Oktoban 2023, lamarin da ya sa aka dakatar da bikin saboda hare-haren Isra’ila a Gaza da Gaɓar Yamma.
Dubban Kiristoci Falasdinawa sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a bainar jama'a a Gaza da aka yi wa ƙawanya da kuma Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye a karon farko tun bayan fara kisan ƙare-dangi a yankin a watan Oktoban 2023.
A cikin shekaru biyu da suka gabata, an dakatar da bukukuwan Kirsimeti a Gaza saboda zaluncin Isra'ila. Ko dai an rufe su ko kuma an soke su gaba ɗaya a Gaɓar Yamma da aka mamaye don nuna goyon baya ga Falasɗinawa a yankin da aka yi wa ƙawanya.
A Bethlehem, wurin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam, dubban mutane sun yi tattaki a kan tituna, tare da bukukuwa cike da murna, suna sanye da kayan Santa Claus suna kiɗa da waƙa.
A Gaza, domin bikin Kirsimeti, Falasɗinawa sun je Cocin Iyali Mai Tsarki, wadda ta lalace sakamakon hare-haren Isra'ila kuma ta zama mafaka ga Falasɗinawa da aka raba da gidajensu.