Butum-butumi ya kafa bajintar duniya a Gasar Tsere ta Beijing
Butum-butumi ya kafa bajintar duniya a Gasar Tsere ta Beijing / AP
Butum-butumi ya kafa bajintar duniya a Gasar Tsere ta Beijing
Wani butum-butumi (humanoid robot) da ya fafata da mutane ya kafa bajintar duniya a gasar gudun sassarfa (wato half-marathon) da aka yi a birnin Beijing ranar Lahadi.

Masu kallo sun cika titunan yankin Yizhuang da ke kudancin babban birnin kasar don kallon yadda injinan da abokan hamayyarsu mutane ke tseren, inda kowane bangare ke gudunsa a layin daban domin kauce wa hadari ko cin karo.

Wasu daga cikin butum-butumi din suna da saurin motsi kwarai, suna gudu kamar fitaccen dan tseren nan Usain Bolt, yayin da wasu kuma kwarewarsu ba ta kai haka ba.

Butum-butumi da suka zama zakara, wanda aka kera da fasahar Autonomous Navigation) kuma yake wakiltar kamfanin wayar salula na kasar China, Honor, ya kammala tseren kilomita 21 a cikin minti 50 da sakan 26. Wannan yana nufin yana gudu a kan gudun kilomita 25 a kowace sa’a, kamar yadda gidan talabijin na CCTV ya ruwaito. Mutumin da ya fi kowa gudu a tseren na ranar Lahadi ya yi baya da minti 17 idan aka kwatanta da lokacin da butum-butumin ya kammala nasa.

Bajintar mutum ta yi baya da kusan minti bakwai

Wannan sakamako ya doke bajintar duniya ta maza na yanzu wadda dan gudun kasar Uganda, Jacob Kiplimo, ke rike da ita na minti 57:20. Wannan sakamakon ya nuna gagarumin ci gaba idan aka kwatanta da bara, inda butum-butumi -masu-gudu suke ta faduwa akai-akai, kuma wanda ya fi kowa kokari ya kwashe sama da sa’o’i biyu da minti 40 kafin ya karasa.

Adadin butum-butumin da suka shiga gasar ya karu daga kusan 20 a bara zuwa sama da 100 a bana, a cewar masu shirya tgasar, wanda hakan ke nuna ci gaban da gasar ta samu.

Han Chenyu, wata daliba mai shekaru 25 da ta kalli tseren, ta bayyana cewa kusan ba ta samu lokacin fito da wayarta don daukar hoton butum-butumin da ke gaba ba saboda yadda ya wuce a guje. Butum-butumin da ya yi nasara tsawonsa santimita 169 ne (wato kafa 5.5), nauyinsa kilogiram 45, kuma an kera shi ne don ya saba da kowane irin yanayi yayin da yake gudu a guje.

Abin da aka saba gani

Ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa tana sha’awar irin wannan ci gaba na fasaha kuma tana ganin taron a matsayin abin “burgewa.” Sai dai ta kara da cewa, “A matsayina na mai neman na kaina, wani lokacin ina dan fargaba. Ina jin kamar fasaha na ci gaba da saurin da har zai iya fara shafar ayyukan mutane,” musamman ganin yadda fasahar kirkirarriyar basira (AI) ke kara bunkasa.

Butum-butumi masu siffar mutum sun zama abin da aka saba gani a kasar China a shekarun nan, a kafafen yada labarai da ma wuraren taron jama’a.

Xie Lei, mai shekaru 41, wanda ya kalli tseren ranar Lahadi tare da iyalinsa, ya ce butum-butumi za su iya “zama bangare na rayuwarmu ta yau da kullum” nan da ’yan shekaru, inda za a iya amfani da su wajen “abubuwa kamar aikin gida, taya tsofaffi hira ko kulawa da marasa lafiya” ko ma “ayyuka masu hadari, har ma da kashe gobara.”

An kara fadada mana tunani”

Gasar gudun sassarfa ta butum-butumi tana da nufin karfafa kirkire-kirkire da kuma bayyana fasahohin da ake amfani da su wajen kerawa da sarrafa irin wadannan injina.

“Tsawon dubban shekaru, mutane ne suka kasance a kololuwa a doron kasa. Amma yanzu, duba butum-butumi. Ta fuskar sarrafa kansu kadai, a kalla a wannan gasar wasanni, sun riga sun fara tsere mana,” in ji Xie.

“A gefe guda, hakan na sa ka dan ji bakin ciki ga bil’adama. Amma a lokaci guda, fasaha, musamman a shekarun nan, ta ba mu damar yin tunani mai fadi kan abin da gobe za ta kasance.”

Duk da haka, hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya (World Athletics) ba za ta amince da bajintar da butum-butumi ya kafa a matsayin bajintar din wasannin mutane ba.