Za a ƙara farashin man fetur a Ghana

Bayanai daga masana’natar mai sun nuna cewa za a kara farashin mai kama daga kashi 1.18 cikin 100 zuwa kashi 3.54 cikin 100, inda za a sayar da ko wace lita ɗaya ta mai kan kuɗi GH¢13.15 (wato naira 1731.90 kuɗin Nijeriya).

By
Rahotanni sun ce ƙrin darajar kuɗin cedi ya taƙaita ƙarin farashin man da ake hasashe

Ana tsammanin masu sayar da mai a ƙasar Ghana su fara ƙara farashin mai a daga ranar Litinin 17 ga watan Nuwamba.

Rahotanni daga ƙasar suna cewa wannan zai faru ne sakamakon nazari na lokaci zuwa lokaci da aka yi game da farashin mai da kuma bayanai game da makomar farashin mai daga ƙungiyar kare muradun masu amfani da mai na ƙasar (COPEC), wadda ta yi hasashen ƙari na kashi 1 zuwa kashi 4 cikin 100 kan kowace litar man fetur.

Kafar JoyFM ta ƙasar ta ambato wasu kamfanonin mai na ƙasar na cewa za su sauya farashin mansu natake yayin da wasu ke cewa za su kalli yadda gogayya za ta kasance a kasuwa kafin su ɗauki mataki.

Dalilai

Rahoton yanayin farashin da COPEC ta fitar ta ce muhimmin abin da zai yi silar ƙarin farashin da ake tsammani shi ne ƙarin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

Farashin ɗanyen mai ya ƙaru da kashi 2.95 cikin 100 a tsakiyar watan Nuwamba shekarar 2025 — daga $62.82 zuwa $64.67 — yayin da ake ƙara alaƙanta barazanar ƙarin farashi da damuwa ta haraji da dakatar da gwamnatin Amurka da kuma sabbin takunkumai kan man Rasha.

Bisa wannan farashin nau’o’i na mai sun ƙaru sosai:

Farashin man fetur ya ƙaru da kashi 3.85 cikin  yayin da Farashin man gas ya ƙaru da kashi 12 cikin 100.

Farashin iskar kuma ya ƙaru n eda kashi 6.97 cikin 100.

Duka da cewa darajar kuɗin ƙasar (cedi) ta dan farfaɗo kwanan nan, darajar da kuɗin ya ƙara bai kai ya hana ƙari a farashin man ba, in ji rahotanni.

Wasu rahotanni sun ce da ba don ƙarin darajar cedi ba, da ƙarin farashin man ya yi yawa a ƙasar.

Rahoton ƙungiyar COPEC ya nuna cewa a lokacin nazari kan farashin daga ranar 16 ga watan Nuwamba na shekarar 2025, cedi ya ƙara daraja daga GH¢11.12 zuwa GH¢10.94 kan dala ɗaya — ƙarin daraja na kasha 1.57 cikin 100.

Farashin da ake tsammanin za a sayar da mai

Bayanai daga masana’natar mai sun nuna cewa ƙarin farashin mai zai karu da kashi 1.18 cikin 100 zuwa kashi 3.54 cikin 100, inda za a sayar da kowace lita ɗaya ta mai kan kuɗi GH¢13.15 (wato naira 1731.90 kuɗin Nijeriya).

Ana tsammanin farashin LPG zai ƙaru da tsakanin kashi 1.32 cikin 100 zuwa kashi 3.53 cikin 100.