An fara Taron Diflomasiyya na Antalya na 2026 inda shugabannin duniya ke halarta
Turkiyya na karbar bakuncin karo na biyar na Taron Diflomasiyya na Antalya, inda ake tattara shugabanni da jagorori daga kasashen duniya sama da 50.
An fara taron karo na biyar na Diflomasiyyar Antalya a Turkiyya a ranar Jumma'a, inda aka tattaro shugabannin duniya da manyan jami'ai domin tattauna hanyoyin magance rashin tabbas da ke karuwa a duniya.
A yayin taron da ake gudanarwa a karkashin jagorancin shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan kuma ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ke daukar nauyin shiryawa, ana gudanar da taron kwanaki uku a birnin Antalya da ke kudancin Bahar Rum wanda a bana yake da taken Bayyana Gobe, Magance da Rashin Tabbas.
Ana wakiltar kasashe sama da 150 a taron, ciki har da shugabannin gwamnatoci sama da 20 da kuma kusan mataimakan shugabanni 15.
Taron ya kuma tattaro ministoci sama da 50 - sama da 40 daga cikinsu ministocin harkokin waje - da kuma wakilai daga kungiyoyi 75 na kasa da kasa.
A jimlace, ana sa ran manyan mahalarta sama da 460 dada cikin kusan mahalarta 5,000 da suka hada da malamai da dalibai.
Mahalarta taron daga Afirka da Turai sun kai kusan rabin shugabannin ƙasashen da suka halarci taron. A lokaci guda, ana sa ran ministocin harkokin waje za su halarta, galibi daga Afirka, Turai da Asiya.
Taron ya ƙunshi kwamitoci da taruka sama da 40, ciki har da tattaunawa tsakanin shugabannin da ke magance ƙalubalen siyasa, tattalin arziki, muhalli, da fasaha, tare da mayar da hankali kan yanayin duniya mai tasocwa.
Ana watsa zaman kai tsaye a shafin yanar gizo da shafukan sada zumunta na taron, tare da wasu da dama da gidan talabijin na TRT na Turkiyya ke watsa wa.
A gefe guda kuma, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan zai halarci jerin taruka, ciki har da Taron Ministocin Harkokin Waje na ƙasashe uku na Balkan, wani zama kan Gaza, wani taro na yau da kullum na ministocin harkokin waje na Ƙungiyar Kasashen Turkawa, da kuma taron Turkiyya-Pakistan-Saudiyya-Masar.