| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Trump ya ce bai shirya yin yarjejeniya ba domin kawo ƙarshen yaƙin Iran
Trump ya bayyana cewa zuwa yanzu sharuɗɗan yiwuwar yarjejeniyar “ba su gamsar ba tukuna” sannan kuma amincewar Iran na watsar da shirinta na mallakar makamin nukiliya na cikin muhimman ginshiƙin yiwuwar yarjejeniyar.
Trump ya ce bai shirya yin yarjejeniya ba domin kawo ƙarshen yaƙin Iran
Trump ya ce akwai yiwuwar Amurka ƙara kai hari Tsibirin Kharg na Iran "kawai don nishaɗi". / Anadolu Agency
6 awanni baya

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce bai shirya yin yarjejeniya da Iran ba tukuna domin kawo karshen yaƙin da ke ƙara ƙazanta a halin yanzu.

Trump a ranar Asabar ya bayyana cewa sharuɗɗan yiwuwar yarjejeniyar “ba su gamsar ba tukuna” kuma ya ƙi bayar da cikakken bayani kan abin da yarjejeniyar za ta buƙata.

“Iran na so ta yi yarjejeniya, ni kuma bana son yin ta saboda sharuɗɗan ba su gamsar ba tukuna,” kamar yadda ya shaida wa NBC News a wata hira ta waya.

Ya ƙara da cewa amincewar Iran na watsar da shirinta na mallakar makamin nukiliya na cikin muhimman ginshiƙi na yiwuwar yarjejeniyar.

Ya bayyana harin Amurka a kan Tsibirin Kharg a matsayin wanda ya “lalata gaba ɗaya” yawancin abubuwan soja na tsibirin. Ya ƙara da cewa “zai yiwu mu sake kai hari wurin kawai don nishaɗi.”

Buɗe Mashigin Hormuz

A wani abu na daban, a cikin wani rubutu a shafin Truth Social ɗinsa, Trump ya rubuta cewa “ƙasashe da dama, musamman waɗanda abin ya shafa dangane da yunƙurin Iran na rufe Mashigin Hormuz, za su aike da jiragen ruwa na yaƙi, tare da haɗin gwiwar Amurka, don ci gaba da buɗe mashigin da tabbatar da amincinsa.”

Ya ambaci China, Faransa, Japan, Koriya ta Kudu, da Birtaniya a matsayin masu yiwuwar turo dakarunsu.

Trump ya kuma ƙara da cewa babu tabbaci ko Iran ta dasa nakiyoyi a Mashigin Tekun.

“Za mu ƙara tsabtace Mashigin da ƙarfi, kuma muna tsammanin wasu ƙasashe za su haɗa kai da mu,” in ji shi.

Bai ba da tabbaci kan ko rundunar sojin ruwa ta Amurka za ta yi wa jiragen ruwan na ‘yan kasuwa rakiya a Mashigin Hormuz ba, sai dai ya ƙara cewa “mai yiwuwa ne.”