Trump ya dakatar da gidan rediyon VOA, ya ba ma'aikatan hutun dole
Tuni Trump ɗin ya soma ɗaukar wasu matakai waɗanda suka haɗa da soke kwantiragin da VOA ɗin ke da shi na amfani da labaran kafafen watsa labarai masu zaman kansu daga ciki har da kamfanin dillancin labarai na Amurka wato AP.
Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump ta dakatar da ayyukan gidan rediyon Muryar Amurka VOA da wasu kafafen watsa labarai na gwamnatin Amurka, inda daraktan na VOA ya sanar da cewa an bai wa kowane ma’aikaci hutun dole.
A ranar Juma’a, jim kaɗan bayan majalisa ta amince da wani kudirin doka, Trump ya bayar da umarni ga gwamnatinsa ta rage ayyukan ma’aikatu da dama kamar yadda doka ta tanada.
Daga ciki har da hukumar US Agency for Global Media wadda gidan rediyon Muryar Amurka wato VOA ke ƙarƙashinta da Radio Free Europe da Asia da Radio Marti wadda ke yaɗa labarai da Sifaniyanci a Cuba.
A ranar Asabar, Kari Lake, wadda Trump ya naɗa a matsayin babbar mai ba shi shawara game da hukumar ta wallafa a shafinta na X kan cewa duk wani ma’aikaci ya duba adreshinsa na email.
Wannan ya zo daidai da labaran da aka rinƙa yaɗawa kan cewa an bai wa ma’aikatan na VOA hutun dole mai albashi.
Gidan rediyon VOA na yaɗa labarai na abubuwan da ke faruwa a cikin Amurka da wajenta zuwa sauran ƙasashe inda ake fassara labaran zuwa harsusan duniya da dama.
Haka kuma tuni Trump ɗin ya soma ɗaukar wasu matakai waɗanda suka haɗa da soke kwantiragin da VOA ɗin ke da shi na amfani da labaran kafafen watsa labarai masu zaman kansu daga ciki har da kamfanin dillancin labarai na Amurka wato AP.