EFCC ta tilasta wa boka dawo da gidaje da motocin da ya damfari wani mutum a Nijeriya

Kayayyakin sun hada da gidaje guda uku, da motoci na alfarma guda biyu da kuma kudi lakadan har naira miliyan daya da dubu dari daya na kafin alkalami, kamar yadda EFCC ta bayyana a shafinta na X.

Daya daga cikin gidajen da aka kwace a hannun bokan. / EFCC

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa, EFCC ta kwato wasu kadarori daga hannun wani boka a birnin Ibadan na jihar Oyo, inda ta damka su ga mutumin da ya damfara.

Kayayyakin sun hada da gidaje guda uku, da motoci na alfarma guda biyu da kuma kudi lakadan har naira miliyan daya da dubu dari daya na kafin alkalami, kamar yadda EFCC ta bayyana a shafinta na X.

Gidajen sun hada da babban gida mai dakuna biyar da baskwata mai daki uku a Ibadan, sai wasu gidajen guda biyu a farfajiya daya masu dakuna uku-uku a Ibadan din, da kuma gida mai daki uku a kauyen Idi Ayunre.

Sauran abubuwan sun hada da mota samfurin Honda Pilot SUV da Toyota Corolla, kuma duka wata mataimakiyar kwamanda ta EFCC ta shiyyar jihar Oyo, Hauwa Garba Ringim ce ta mika wa mai kayan Daniel Babatunde Attiogbe, a madadin Shugaban hukumar Ola Olukoyede. 

A yayin da take mika masa takardu da makullan kadarorin, wakiliyar EFCC ta ce an bai wa mai kayan abubuwansa da aka kwato din ne ne bisa umarnin kotu.

“Bin umarnin kotu ya zama wajibi kuma a matsayinmu na hukumar gwamnatin tarayya, mun san muhimmancin abin da muka aiwatar ke nan a yau. Kuma hakan alama ce da ke nuna cewa EFCC tana gudanar da ayyukanta bisa tsarin doka.

Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Ibadan, Uche Agomoh ne ya ba da umarnin kwato kadarorin tare da bai wa masu su a hukuncin da ya yanke a watan Nuwamban 2024, a shari’ar da aka fara ta a 2019.

Alkalin ya kama bokan mai suna Olalere Alli da laifin hada kai da wasu yaransa inda suka damfari Daniel kudi fiye da miliyan 200 da nufin zai masa asiri don hana shi mutuwa lokacinsa bai yi ba.

Da farko an fara tuhumar bokan ne da laifuka 33, amma daga baya sai aka mayar da tuhumar guda daya.

Bayan kwace kadarorin, an kuma yanke wa Boka Alli hukuncin daurin shekara uku a gidan yari da kuma saka shi yin alkawari a gaban hukumar tsaro ta farin kaya, DSS cewa zai gyara halayensa kuma ba zai sake yin wani mummunan aiki ba.