| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Boko Haram ta ƙona wasu makarantun firamare da sakandare a Jihar Borno
Lamarin na zuwa ne bayan an sace ɗaliban makarantar Firamare da Sakandare ta Mussa da ke Askira-Uba kusan wata guda da ya gabata, ba tare da an gano inda suke ba.
Boko Haram ta ƙona wasu makarantun firamare da sakandare a Jihar Borno
Jihar Borno na daga cikin jihohin da aka shafe tsawon shekarau ana fama da matsalar tsaro a Nijeriya / Reuters

Wasu da ake zargin ’yanta’addan Boko Haram ne sun ƙone makarantun firamare da sakandare da ke ƙauyen Kautikari a Ƙaramar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.

Lamarin na zuwa ne bayan an sace ɗaliban makarantar Firamare da Sakandare ta Mussa da ke Askira-Uba kusan wata guda da ya gabata, ba tare da an gano inda suke ba.

Majiyoyin tsaro sun ce maharan sun kai farmaki garin da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar Asabar. Garin dai ya sha fama da hare-hare a lokuta da dama a baya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

 “Ya zuwa yanzu ba a samu asarar rai ba, amma mazauna yankin sun tsere zuwa cikin daji domin neman tsira,” in ji ɗaya daga cikin majiyoyin.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ’yanta’addan sun kai hari ƙauyen watanni da suka gabata, amma ba su lalata wata kadarar gwamnati ko ta masu zaman kansu ba.

“Abin mamaki ne yadda suka ƙone makarantar firamare da makarantar sakandaren jeka-ka-dawo. Irin wannan hari ba kasafai ake ganin sa ba,” in ji shi.

Duk ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda, ASP Nahum Kenneth Daso, bai yi nasara ba, domin wayarsa ba ta shiga, a cewar jaridar.

 

 

Rumbun Labarai
'Yansandan Nijeriya sun kama Adeniyi wanda ake zargi da kafa hukumar bogi
Nijeriya da Masar na shirin karfafa hadin gwiwa a yaki da miyagun kwayoyi
Matsalar ta'ammuli da miyagun ƙwayoyi tsakanin mata a Nijeriya
Matatar Dangote ta koma amfani da farashin dala don sayar da manta maimakon naira
'Yanbindiga sun kashe mutane aƙalla 18 a Jihar Benue da ke tsakiyar Nijeriya, in ji mazauna yankin
Abin da zuwan kasuwar hannun-jarin Nijeriya ta farko a duniya ke nufi
Ɗanyen man da Nijeriya ke samarwa ya kai matakin da ya fi yawa tun watan Yunin 2020
Sojojin Nijeriya sun kashe mai ɗaukar bidiyon ISWAP da gano wasu Larabawa masu horas da ‘yanta'adda
NDLEA ta kama 'yar Afirka ta Kudu kan zargin amfani da ɗanta mai shekara 3 wajen safarar hodar iblis
Hare-haren saman sojin Nijeriya sun kashe gomman 'yanta'addan Boko Haram
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda' fiye da 300 a Zamfara
Jami'an tsaron Nijeriya sun ceto daliban da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo
Nijeriya ta zo ta farko a duniya a tagomashin kasuwar hannun-jari
Wasu da ake zargi ’yan ISWAP ne da iyalansu sun miƙa wuya ga sojojin Nijeriya
Matatar mai ta Dangote ta fara dakon fetur kyauta zuwa wasu jihohin Nijeriya
Majalisar Dattawan Nijeriya ta buƙaci a soke shirin gyaran hali na tubabbun 'yan Boko Haram
Jihar Legas ta kama mabarata 396, tana tantance bayanansu domin mayar da su jihohinsu na asali
Nijeriya za ta binciki manyan kamfanonin fasaha kan amfani da labaran ƙasar ba bisa ƙa’ida ba
Gwamnatin Nijeriya ta bai wa 'yan ƙasarta damar ƙarshe ta kwashe su daga Afirka ta Kudu
‘Yansandan Nijeriya sun dakile harin ‘yanbindiga a Sokoto