Akalla mutum 25 ne suka rasa rayukansu a hare-haren 'yan ta'adda guda biyu a jihar Adamawa, arewa-maso-gabashin Nijeriya, in ji kamfanin dillancin labarai na AFP yana ambato jami'an jihar.
Ana zargin kungiyar Boko Haram ce ta kai hare-haren garuruwan Madagali da Hong a yankin kan iyaka da Kamaru.
"'Yan bindiga da muke zaton 'yan Boko Haram ne kan babura da yawa... sun kai farmaki kasuwa. Sun bude wuta kan mutane suka hallaka 21," wani jami'in gwamnati na Madagali ya shaida wa AFP game da harin na ranar Talata da yamma, amma ya nemi a sakaya sunansa.
"Har yanzu muna neman ƙarin gawawwaki domin ta iya yiwuwa wasu da suka ji raunuka sakamakon harbin bindiga a daji suka mutu yayin da suke kokarin neman mafaka."
Sata a kasuwa
Masu kai harin sun kum yi sata a kasuwa; sun ƙwace kayayyakin abinci da babura, in ji wannan majiya.
Mutane hudu kuma, ciki har da sojoji uku ne suka mutu a Hong, in ji wani mazaunin garin Ezekiel Musa kamar yadda ya shaida wa AFP.
"Boko Haram sun kai mana hari bayan sun bar garin. Mun ga gawar sojoji uku kuma an kashe wata mata," in ji Musa. "Yanzu gari na da jami'an tsaro amma wasu daga cikinmu sun riga sun fara barin garin saboda tsoron abin da ya faru."
Gwamnan jihar Adamawa, Adamu Umaru Fintiri, ya yi Allah wadai da harin a cikin wata sanarwa, ba tare da ya faɗi yawan waɗanda suka mutu ba a hukumance.
"Ba za mu bar 'yan ta'adda su raunana yunƙurinmu na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba," ya ce a sanarwar.
"Ina gargadi ga masu aikata wannan: ku daina irin ire-iren wadannan hare-hare marasa ma'ana ko kuma ku fuskanci dukkan ƙarfin azamarmu ta hadin-kai."
Tun daga shekarar 2009, hare-haren Boko Haram da 'yan ta'addan da ke da alaka da Daesh sun jyi sanadin mutuwar fiye da mutum 40,000 da kuma zama sanadin yin gudun hijirar kusan miliyan biyu a arewa-maso-gabas na kasar, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Nijeriya ma tana fama da sauran kungiyoyin makamai wadanda suka ƙara jawo taɓarɓarewar matsalolin rashin tsaro a arewacin kasar.















