Kisan-gilla biyar da suka tayar da hankali a Kano
Duk da cewa a faɗin Nijeriya ana samun rahotannin kisan kai akai-akai, amma irin waɗanda ake samu a Kano na jan hankali saboda abubuwan da ke tattare da kisan musamman na ban al’ajabi ko tsananin tausayi ko kuma wani abu da hankali bai cika ɗauka ba.
A ‘yan shekarun nan, ana yawan samun rahotannin kisan-gilla a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya inda akasari kisan ke tayar da hankalin jama’a.
Duk da cewa a faɗin Nijeriya ana samun rahotannin kisan kai akai-akai, amma irin waɗanda ake samu a Kano na jan hankali saboda abubuwan da ke tattare da kisan musamman na ban al’ajabi ko tsananin tausayi ko kuma wani abu da hankali bai cika ɗauka ba.
Dangane da irin waɗannan abubuwa, TRT Afrika Hausa ta yi nazari dangane da kisan-gilla biyar da suka yi matuƙar tayar da hankali a Kano.
Kisan Fatima Abubakar da ‘ya’yanta shida
A ranar Asabar, 17 ga Janairun 2026 ne aka samu rahoton kisan Fatima Abubakar mai shekara 35 a unguwar Dorayi Charanchi da ke cikin birnin Kano tare da ‘ya’yanta shida.
Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ana zargin maharan da amfani da muggan makamai wurin aikata wannan ta’asar.
Bayan samun wannan rahoto, kafofin sada zumunta sun ɗauki ɗumi matuƙa inda ake ta alhinin faruwar wannan mummunan lamari da addu’ar kamo waɗanda ake zargi da aikata ta’asar da hukunta su.
Sai dai a safiyar Lahadi rundunar ‘yan sandan ta fitar da sanarwa inda take tabbatar da kama mutum uku waɗanda ake zargi da kisan.
A yayin samamen, ‘yansandan sun gano tufafi masu ɗauke da jini, makamai, da kayayyakin da aka sace, yayin da bincike ke ci gaba.
Kisan Nafiu a Kano
Kisan da ake zargin wata matar aure mai suna Hafsat ta yi wa wani matashi a Jihar Kano mai suna Nafiu Hafiz a shekarar 2023 ya jawo ce-ce-ku-ce a lokacin da lamarin ya faru sakamakon yadda aka rinƙa samun bayanai daban-daban da suka rinƙa fitowa masu daure kai.
Rahotanni sun nuna cewa wadda ake zargin wato Hafsat, da ita da mijinta iyayen gidan marigayin ne, kuma abin ya faru ne a gidansu da ke Unguwa Uku a Kano.
Labarin kisan Nafiu dai ya karaɗe shafukan sada zumunta a faɗin Nijeriya, kuma batun ya ɗauki hankali sosai inda ya jawo ce-ce-ku-ce da Allah wadai daga faɗin ƙasar.
Kisan Hanifa
Kisan Hanifa wadda yarinya ce mai shekara biyar a Kano ya yi matukar tayar da hankalin jama’a sakamakon yadda lamarin ya kasance mai ban tausayi da takaici.
Bayan kisan Hanifa, Babbar Kotun Kano ta yanke wa malaminta Abdulmalik Tanko hukuncin kisa bayan samunsa da laifin garkuwa da Hanifa da laifin kisanta da kuma laifin kitsa yadda za a yi garkuwa da ita.
Tun da farko malamin na su Hanifa ne ya hada kai da wasu domin sace ta inda daga baya ya kashe ta sannan ya binne ta a cikin wani buhu.
Sai dai tun bayan yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa, babu wani karin bayani game da aiwatar da hukuncin na kisa a kansa.
Ummita da Dan China
A shekarar 2022 ne aka zargi wani dan kasar China mai suna Geng Quangron da kashe budurwarsa mai suna Ummulkulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.
Shi ma wannan lamarin ya tayar da kura wanda hakan ya sa aka shafe makonni ana tafka muhawara a shafukan sada zumunta.
A lokacin da lamarin ya faru, an zargi dan kasar Chinan da bin Ummita har gidansu da ke unguwar Janbulo inda ya soka mata wuka wanda hakan ya yi ajalinta.
Daga baya an gurfanar da Mista Geng a gaban kotu inda ya amsa laifin kisan Ummita tare da cewa ya kashe mata kudi fiye da naira miliyan 60.
Mahaifiyar da ta kashe ‘ya’yanta biyu a Kano
A watan Oktoban 2020 ne kuma aka shiga wani hali na ruɗu a birnin Kano, bayan da aka yi zargin wata uwa da kashe ƴaƴanta har biyu a Unguwar Sagagi.
Rundunar ƴansandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar yaran, Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da 'yar uwarsa Zahra'u Ibrahim mai shekara uku.
A shekarar 2020 ne wani lamari mai kama da almara wanda ya matukar jawo ce-ce-ku-ce ya faru a unguwar Sagagi a Kano bayan wata mata ta kashe ‘ya’yanta biyu.
Ana zargin matar da kashe ‘ya’yanta biyu wadanda suka hada da Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da Zahra’u Ibrahim mai shekara uku bayan mijin ya yi barazanar yi mata kishiya.
Sai dai a bayanin da iyayen matar suka yi wa ‘yan sanda, sun ce ‘yarsu na da tabin hankali tsawon shekaru