Sojojin Ruwan Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran sun bayyana cewa wani babban jirgin dakon man fetur ya taka nakiya a Mashigar Hormuz, lamarin da ya haddasa gagarumar gobara.
Jirgin na ɗauke da ganga fiye da miliyan biyu na ɗanyen mai a lokacin da yake ƙoƙarin wucewa ta mashigar, a cewar wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya wallafa.
Rundunar sojin ruwan ta bayyana jirgin a matsayin jirgin dakon mai wanda ya saɓa ƙa’ida da yin gaban kansa ta hanyar kashe na’urar radar ɗinsa wadda ke bayar da dama a bi diddiƙinsa.
Ta yi zargin cewa jirgin ya yi ƙoƙarin amfani da tallafin sojin Amurka wajen jigilar kayayyaki ta mashigar ruwan.
Mashigar Ruwan Hormuz na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya, inda kaso mai tsoka na man da ake sayarwa a kasuwannin duniya ke bi ta cikinsa.
Muhimmancin mashigar ya sa ta kasance wurin da ake samun takun-saka tsakanin Iran da Amurka, lamarin da ke haifar da fargabar tasirin duk wani rikici a yankin ga samar da man fetur da farashinsa a duniya.






















