Me ya sa Kannywood ke fafutuka yayin da Nollywood ke samun tagomashi?
NIJERIYA
6 minti karatu
Me ya sa Kannywood ke fafutuka yayin da Nollywood ke samun tagomashi?Masana'antar fina-finan Hausa da ke Nijeriya tana fuskantar matsaloli kamar ƙarancin gidajen silima, sa-ido kan kiyaye al'adu rashin wadatar kafofin dijital.
Me ya sa Kannywood ke fafutuka yayin da Nollywood ke samun tagomashi? / Others
6 awanni baya

"Za ka iya haɗa fim, amma babu inda za ka kai shi."

Masana’antar fim da ke kudancin Nijeriya tana samun karɓuwa a kasuwar fim ta Amurka da zuba jari daga Netflix da Amazon Prime, amma a cewar wani sananne ɗan Kannywood, Sani Mu'azu yana kwatanta masana’antar a wani irin yanayi ɗungurungum.

Kannywood ita ce masana’antar fim ta Nijeriya ta harshen Hausa, amma fina-finanta ba sa samun karɓuwa a gidajen silima na duniya.

Mu'azu, mai shirya fim, darakta kuma tsohon babban shugaban ƙungiyar masu harkar fim ta Nijeriya, Motion Picture Practitioners' Association of Nigeria. Ya kwashe sama da shekaru talatin a Kannywood, inda ya ga tasowarta har take iya fitar da ɗaruruwan fina-finai duk shekara.

Ya shaida yadda masana’antar da ringa rasa kimarta yayin da Nollywood ke ci gaba da haɓaka.

"Ya kamata silima ta ba ka damar maida kuɗi," in ji Mu'azu a zantawa da TRT Afrika. "Idan ba ka samu silima ba, ba za ka iya mai da kuɗinka ba. Kenan, Kannywood ba za ta iya shirya fim mai tsada ba."

Tabbas, tsawon shekaru tattaunawa kan fina-fianan Nijeriya ta karkata kan ɓangaren Nollywood da ke kudanci – inda ake haɗa fim na miliyoyin naira kuma ake gabatar da fina-finan a silimomin birnin Lagos.

Nesa da inda ake cin kasuwar nan, Kannywood tana fama da neman tsira daga saka-ido, , masu bugun jabu, da ra’ayin riƙau na al’adu.

A yanzu, tana fuskantar babban ƙalubale na yadda za ta zamanantar da aiki zuwa dijital, da samun masu kallo a duniyaba tare da ta rasa kamannin a’adun da aka san ta da shi ba.

"Kannywood babban ɓangare ne na Nollywood," a cewar Mu'azu. "Nollywood ta faro ne daga ziro har ta zama mafi girman masana’antar fim a duniya. Kannywood ɓangare ne na wannan tafiyar. Yawan fina-finai kawai yana nuna masu son nuna bajintarsu."

Kamar Nollywood, Kannywood ta taso daga ƙasa ba wai tallafin gwamnati ba. Masu shirya fim na farko sun dogara kan kaset na VHS, sai VCDs da DVDs wajen sayar da fim a manyan kasuwannin Kano kamar Kofar Mata da Bata. Waɗannan ne manyan kasuwanni sayar da fim a arewa.

A kudanci ana da kasuwannin sayar da fim a Idumota da Alaba a Lagos, inda Nollywood take ƙara samun ƙwarewa a hanyoyin aiki da faɗaɗa kasuwa a duniya. Ita kuwa Kannywood tana neman tsira.

Bambancin ya ƙara bayyana a ‘yan shekarun nan. Bayanai daga ƙungiyar masu nuna fim a silim ta Nijeriya sun nuna masana’antar fim a ƙasar ta samar da naira biliyan 11.5 (dala US miliyan $8.4) a kuɗin-shiga a 2024, da ƙarin kashi 60% a bara.

Mafi rinjayen cigaban ya zo ne daga kudu, inda ɗaruruwan silima ke taimakon fim mai tsada. Idan an kwatanta da Arewacin Nijeriya ‘yan tsirarun silima ne ke aiki. Wasu ma sun rufe.

Tazarar fasaha

Matsalolin Kannywood sun fi bayyana a kafofin dijital. Yayin da Netflix da Amazon Prime suke ba da wadataccen gurbi ga fina-finan kudancin Nijeriya, da wuya ka ga wani fim na Hausa.

Sakamakon raguwar adadin silima da ƙarancin damar saka fim a kafofin nuna fim na zaɓi-sonka, yawancin masu shirya fim a Kannywood suna komawa YouTube, inda samun kuɗi ya dogara kan tsarin intanet maimakon ginannen tsarin silima. Sai kuma batun masu buga jabun fim.

"Masu buga jabu suna saukewa da yaɗa fina-finanmu ga mutane don samun kuɗi. Maishirin fim bai san komai ba game da keta haƙƙoƙinsa na mallaka da wasu ke yi suna samun kuɗi," in ji Sani Mu'azu.

Kannywood tana da ɗumbin mabiyan da ke sha’awar kallon fina-finanta sama da miliyan 80 a faɗin Yammaci da Tsakiyar Afirka da mutane mazauna ƙasashen duniya masu jin Hausa, amma hakan bai samar da riba gare su ba.

Mu'azu ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "‘Yan arewacin Nijeriya ba su kai yawan amfani da intanet ba kamar na kudanci. Kuma ko da waɗanda ke hawa intanet, akwai da yama da ba sa biyan kuɗi don kallon fim ba."

Sabbin shirye-shirye kamar Arewaflix, wata kafar kallon fim ta intanet mai nuna fim da fassarar take a harsuna, alama ce ta ƙaruwar fahimtar cewa dole Kannywood ta riƙe makomarta a fannin dijital. Sai dai Mu'azu ya nemi a yi kaffa-kaffa.

Ya ce, "Akwai kasuwa tanan nan, amma amfani da intanet a arewa ba ya ƙaruwa kamar na sauran ɓangarorin ƙasar."

Sa-idon gwamnati

Kafin Kannywood ta kamo Nollywood, Mu'azu yana ganin dole sai gwamnati ta shigo. Ana buƙatar manufofi masu taimaka wa zuba jari, da tallafin gina silima, da inganta ƙwarewa da wayar da kai game da harkokin dijital a masana’antar.

Sai dai kuma, akwai matsalar rashin tsaro da ke shafar harkar. A wurare da yawa a yankin arewacin Nijeriya, akwai matsalar satar mutane, fashin daji, harin ‘yan-ta’adda da uska mayar da zuba jari a harkar nishaɗi ta zama mai haɗari.

"Ba mai son zuwa kallon fim a yanayi waje da mutane ke son komawa gida tun ƙarfe 6 na yamma," a cewar Mu'azu.

Kafin al’adar zuwa silima ta samu karɓuwa dole masu kallo su samu aminci, kuma wannan amincin ne ba a samu. A birane da dama, harkokin kasuwanci kan ragu da zarar ta magariba ta yi, amma fita neman nishaɗi abu ne da ba dole ba idan yana da haɗari, maimakon mayar da shi abin yau-da-kullum.

A 2018, ‘yan bindiga sun kai hari silima a jihar Zamfara, inda suka kashe mutum 11 suka kuma jikkata wasu sama da 20.

Mua’azu ya ƙara da cewa, "Mun yi ƙoƙarin janyo hankalin masu zuba jari daga Lagos, amma rashin tsaro ya zama tarnaƙi. Ta yaya za ka zuba jari bayan babu wanda yake da tabbas?"

Sabon salan labari

A yanayin irin wannan rashin tabbas, masu shirya fim suna gwada shirya gagaruman fina-finan tarihi, da na sharhi kan zamantakewa, da masu jinjinawa Nijeriya waɗanda za su burge masu kallo da ke wajen yankin arewacin ƙasar.

Fim ɗin da Mu'azu ke shiryawa wanda zai fito nan gaba, mai suna Gamji Zone, an shirya a yanayin shekarun 1960 kuma ya nuna rayuwar soyayya tsakanin wani Bahaushe da wata Bafulatana yayin da ake yaƙin basasa, da batun nuna-kai, da kishin ƙasa, ta mahangar soja ɗan ƙabilar Igbo.

Da yake jawabi kan fim ɗin nasa, Mu’azu ya ce, "Ba wai labarin soyayya ne kawai ba, fim ɗin ya shafi batun fahimtar Nijeriya a matsayin ƙasa mai al’ada guda duk da bambance-bambancen al’ummarta."

Kannywood na tsaka mai wuya tsakanin neman tsira da neman cika buri. A halin yanzu tana kan samun sauyi, akwai tarin fikirori amma raunin arziƙi, giɓin manufofi, da yanayin al’adu.

"Duk da cewa akwai gagarumar dama, Kannywood ba ta kai inda ya kamata ta kai ba," in ji Sani Mu'azu.