Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya sanar da yin murabus bayan shan matsin lamba kan jagorancinsa tsawon watanni. Murabus ɗin ya haifar da wani mataki da zai kawo Birtaniya ta samu firaministanta na bakwai a cikin shekaru goma.
A wani jawabi a wajen ofishinsa na 10 Downing Street, Starmer wanda ya hau mulki tun Yuli 2024, ya amince a ranar Litinin cewa ya rasa goyon bayan 'yan majalisar jam'iyyarsa ta Labour.
Ya ce ya shaida wa Sarkin Charles III shawararsa ta yin murabus domin a zaɓi sabon shugaban jam’iyyar Labour, wanda hakan zai sa a zaɓi sabon firaminista.
"Zan ci gaba da kasancewa a matsayin firaminista har sai takara ta kammala, sannan zan yi duk abin da zan iya don tabbatar da miƙa mulki cikin tsari," in ji shi.
Ikon Starmer ya fara raguwa tun bayan da Labour ta yi asarar kujeru a zaɓukan ƙananan hukumomi da na yankuna a watan Mayu.
Ba zai iya jure ƙarin wannan matsin lamba ba, bayan tabbatarwa a makon da ya gabata cewa abokin adawarsa, Andy Burnham zai koma majalisa, abin da ya buɗe ƙofar samun gogayyar shugabanci.
Jadawalin maye gurbi
Andy Burnham, ɗan siyasa ne mai gogewa na Labour, ya shirya karɓar kujerarsa a Majalisar Wakilai ranar Litinin, bayan ya ci zaɓen cike gurbi a gundumar Makerfield, a arewa maso yammacin Ingila, ranar Alhamis.
"Tambayar da jam'iyyata ke yi yanzu ita ce ko ni ne mafi dacewa don jagorantar mu zuwa zaɓukan gamagari na gaba," in ji Starmer, yayin da manyan abokan aikinsa na ministoci ke zura masa ido.
"Na ji amsar jam'iyyata ta majalisa ga wannan tambaya, kuma na karɓi wannan amsa da ladabi.
Cikin jawabi mai motsa rai, ya ƙara da cewa, "Duk shawarar da na yanke ta kasance ne don sanya ƙasar da nake so a gaba. Shi ya sa zan yi murabus a matsayin shugaban Jam'iyyar Labour".
Starmer ya ce ya roƙi Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na Labour ya fayyace jadawalin maye gurbin sa, inda za a buɗe ƙofar karɓar takardun nema a ranar 9 ga Yuli.
"Wannan zai tabbatar da cewa sabon shugaba ya kasance kafin majalisa ta dawo a watan Satumba" bayan hutun lokacin zafi, in ji shi.
Yanzu hankali ya koma kan ko Andy Burnham zai zama shugaba ba tare da hamayya ba, kamar yadda yawancin 'yan majalisar Labour suka nema, ko kuma wani ɗantakara kamar tsohon ministan lafiya Wes Streeting zai yanke shawarar yin takara.
A ƙarƙashin ƙa'idodin Labour, dole ne shugaban jam'iyyar ya kasance mamba na majalisa.
"Damar ƙarshe"
Duk da cewa Keir Starmer ya dage kan cewa zai yaƙi duk wani yunƙurin korar sa, ƙarfin nasarar Burnham a makon da ya gabata da kuma ƙarin matsin lambar da ya biyo baya sun zama masu nauyi sosai.
Sakataren Harkokin Waje, Yvette Cooper da ministan makamashi, Ed Miliband na cikin manyan ministoci da suka shaida wa shugabansu ya tafi, a cewar jaridu, yayin da fiye da 100 daga cikin 'yan majalisar 403 na Labour suka roƙe shi ya yi murabus.
Burnham, wanda ya zama magajin garin Greater Manchester a 2017, ya bayyana a fili cewa yana shirin neman shugabancin Labour, yana gargadin yayin jawabin nasarar zaɓen cike gurbi cewa, jam'iyyar mai mulki da ke fama tana da "damar ƙarshe don canjawa".
Idan Andy Burnham, mai shekara 56 ya yi nasara, zai maye gurbin Keir Starmer a matsayin firaminista sakamakon gagarumin rinjayen da Labour ke da shi a majalisa.












