Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Nijeriya, NEMA, ta karɓi ’yan ƙasar 180 da aka mayar da su gida daga Benghazi ta ƙasar Libya ƙarƙashin shirin Dawowa Bisa Son Rai Tare da Taimako (AVR).
’Yan Nijeriya da aka dawo da su sun isa filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja, Legas, inda ofishin ayyukan NEMA na Legas ya tarbe su tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira, ’Yan Ci-rani da ’Yan Gudun Hijira a Cikin Gida, NCFRMI.
Tawagar ta ƙunshi manya 169 — maza 68 da mata 101 — da kuma yara maza shida, jarirai biyar da kuma mutum ɗaya da ke fama da rashin lafiya.
Ƙungiyar Ƙasa da Ƙasa ta Kula da ’Yan Ci-rani, IOM, ce ta jagoranci shirin dawo da mutanen tare da haɗin gwiwar gwamnatin Nijeriya.
Bayan isowarsu, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya, NIS ta yi musu rajistar bayanan halittar jiki da kuma tantance takardunsu domin sauƙaƙa gano su, adana bayanansu da kuma shirin sake mayar da su cikin al’umma.
An tallafa wa waɗanda aka dawo da su
An ba ’yan Nijeriya da aka dawo da su agajin gaggawa na jinƙai, ciki har da abinci, ruwan sha, duba lafiyar jiki da kuma motocin asibiti ga waɗanda ke buƙatar kulawar lafiya.
Haka kuma, an taimaka musu wajen ɗaukar kayayyakin da suka zo da su da sauran abubuwan da suka shafi zirga-zirga.
An kuma samar da masu ba da shawara da kuma taimakon sake haɗa su da al’ummominsu, domin taimaka musu komawa cikin al’umma cikin aminci.
Hukumomin gwamnati da abokan hulɗar ci gaba daban-daban ne suka gudanar da aikin, da nufin tabbatar da cewa an tarɓi ’yan Nijeriya da aka dawo da su cikin aminci, tsari da mutunci.



















