| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Masu shiga tsakani suna fafutukar kwantar da tankiya tsakanin Amurka da Iran
Kasar Qatar, Saudiyya, Pakistan da Masar suna gudanar da tattaunawa ta wayar tarho mai zurfi da ƙasashen Amurka da Iran domin kwantar da sabuwar taƙaddamar da ta ɓarke, da samar da hanya ga sabuwar tattaunawa ta ƙwararru kan yarjejeniyar nukiliya.
Masu shiga tsakani suna fafutukar kwantar da tankiya tsakanin Amurka da Iran
Majiyoyin sun ce jami’ai daga kasashen Qatar, Pakistan, Masar, da Saudiyya sun gudanar da tattaunawa da jami’an Amurka da na Iran / reuters

Masu shiga tsakani a yankin Gabas ta Tsakiya suna ƙoƙarin sassauta zaman tankiyar da ke ruruwa tsakanin Amurka da Iran, yayin da suke kiran da a ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliya, kamar yadda shafin labarai na Axios ya ruwaito ranar Alhamis.

Majiyoyi da dama, guda biyu daga ƙasashen da ke shiga tsakani sannan guda ɗaya kuma jami’in Amurka, sun shaida wa kafar yaɗa labaran cewa gwamnatocin yankin suna ta ƙoƙarin kwantar da tarzoma tsakanin ƙasashen biyu.

Wata majiya ta shiyya daga ɗaya daga cikin ƙasashen da ke shiga tsakani ta bayyana cewa, masu shiga tsakanin sun yi amannar cewa hare-haren da Iran ta kai a baya bayan nan a Mashigar Tekun Hormuz, wasu ɓangarori ne na cikin gwamnatin Iran da ke adawa da yarjejeniyar tsakanin Amurka da Iran suka kai su, kuma suna neman lalata yarjejeniyar ne.

Majiyoyin sun ce jami’ai daga ƙasashen Qatar, Pakistan, Masar, da Saudiyya sun gudanar da tattaunawa ta wayar tarho da dama da jami’an Amurka da na Iran a ranar Laraba, a matsayin ƙoƙarin kwantar da rikicin.

“Akwai gagarumar fafutuka ta diflomasiyya da farko domin cim ma daidaito da ɓangarorin biyu kan kwantar da tarzoma, sannan daga baya a tsaida lokaci don gudanar da wani zagaye na tattaunawa tsakanin ƙwararru na ɓangarorin biyu,” in ji wata majiya ta shiyya da ke da hannu a shiga tsakanin.

Iran da Amurka sun yi musayar hare-hare a cikin kwanaki biyu da suka gabata, a daidai lokacin da taƙaddama ta ƙazance biyo bayan hare-haren da Iran ta kai kan wasu jiragen ruwa na kasuwanci guda uku a Mashigar Tekun Hormuz.

Gwamnatin Iran ta ƙaddamar da jerin hare-hare a ranar Alhamis kan dakarun sojin Amurka da ke ƙasashen Bahrain, Kuwait, Qatar, da Jordan, a matsayin maida martani ga hare-haren dare da Amurka ta kai musu har na tsawon kwanaki biyu a jere.