Yahudawa ‘yan-kama-wuri-zauna fiye da 65,000 ne suka shiga harabar Masallacin Ƙudus ba bisa ƙa’ida a Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye a shekarar 2025, lamarin da ya nuna ƙari na kashi 22 cikin 100 idan aka kwatanata da shekarar 2024, in ji wani rahoto.
An wallafa aƙalluman ne a wani rahoton shekara-shekara na Gidauniyar Birnin Ƙudus ta ƙasa da ƙasa, waɗanda aka haɗa bisa ƙididdigar da aka samo daga kwamitin Waqf na Musulunci na gudanarwa a Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye.
Rahoton ya ce mutum 65,364 sun shiga wurin cikin shekara ɗaya yayin da ziyara mai alaƙa da ‘yan siyasar Isra’ila ta kuma ƙaru sosai.
Gidauniyar ta bayyana cewa Minsitan Tsaron Cikin Gida na Isra’ila mai ra’ayin riƙau Itamar Ben-Gvir, yana cikin ‘yan siyasar da ke kutsawa cikin harabar tare da wasu ‘yan majalisar.
Adadin irin waɗannan kutse na siyasa sun ƙaru daga tara a shekarar 2024 zuwa 20 a shekarar 2025.
Rahoton ya ce hukumomin Isra’ila sun fitar da sabbin matakai da ke tasiri kan iya shiga wurin ciki har da iya adadin awannin ziyara da ƙara adadin gungun masu shiga daga mutum 120 zuwa mutum 200.
An bayyana waɗannan matakan a matsayin ƙoƙarin sauya daɗaɗɗiyar matsayar harabar mai tsarki da kuma gindaya sabon yanayi a wurin.
Baya ga abubuwan da ke faruwa a Masallacin Ƙudus, rahoton ya ce manufofin Isra’ila da ke da alaƙa da ƙwace takardun zama da na shaida a Birnin Ƙudus ya ci gaba, yana mai tuna cewa Falasɗinawa 14,929 sun rasa katin shaidarsu ta zama tsakanin shekarar 1967 zuwa shekarar 2024.
Ya kuma bayyana matsin lamba mai alaƙa da ilimi, yana cewa ƙarancin kimanin ajujuwa 1,500 a Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye inda ya tabbatar da cewa kimanin kashi 27 cikin 100 na ɗalibai Falasɗinawa ‘yan shekaru 6 zuwa 17 aka shigar cikin manhajar karatun Isra’ila.
Gidauniyar ta yi gargaɗin cewa lokacin da ake ciki a halin yanzu na nuna wani lokacin sauyi a kan abin da ta bayyana a matsayar ƙoƙarin mayar da hankali kan fasalin Birnin Ƙudus, tana mai nuni ga abin da ta siffanta a matsayin manufofin “Yahudantarwa” .
Ta ƙara da cewa kimanin kashi 77 cikin 100 na iyalai a Gabashin Birnin Ƙudus da aka yi wa ƙawanya suna rayuwa ne cikin talauci.
Rahoton ya nuna ra’ayoyin Falasɗinawa cewa Isra’ila tana gaggauta matakai na sake fasalin Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye, ciki har da harabar Masallacin Ƙudus, da kuma goge alamun Larabawa da na Muslunci na birnin.
Falasɗinawa da ke ishara ga ƙudurorin ƙasashen duniya da ba su amince da mamayar da Isra’ila ta yi wa birnin a shekarar 1967 ba ko kuma yadda ta karɓe iko da shi a shekarar 1980, sun ci gaba da kallon Gabashin Birnin Ƙudus a matsayin babban birnin ƙasar Falasɗinawa da za a samar nan gaba.
Bayanan Isra’ila kuwa sun nuna adadin da ya zarce haka, inda suka ce “Yauhudawa masu ziyara” 76,448 sun shiga harabar a shekarar 2025, abin da ya kai ƙarin kashi 31 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.














