Ce-ce-ku-ce bayan dakatar da Sheikh Alƙali Zaria daga Tafsirin Ramadan a Nijeriya
NIJERIYA
3 minti karatu
Ce-ce-ku-ce bayan dakatar da Sheikh Alƙali Zaria daga Tafsirin Ramadan a NijeriyaMatakin da Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah ta ɗauka kan malamin ya janyo muhawara a tsakanin ‘yan Nijeriya kan rawar da malamai ya kamata su taka a batutuwan siyasa da tsaro.
Kafin dakatarwar, malamin ya kwashe kusan kwanaki 11 yana gabatar da tafsirin Ramadan na bana a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe. / Others
5 Maris 2026

’Yan Nijeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan dakatar da wani babban malamin addinin Musulunci daga gabatar da tafsirin azumin watan Ramadan a garin Damaturu da ke Jihar Yobe.

Ƙungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah, wadda aka fi sani da Izala, ce ta dakatar da Sheikh Alƙali Abubakar Salihu Zaria a farkon makon nan. Ƙungiyar ta ce matakin ya biyo bayan kalaman da malamin ya yi a yayin tafsirin da take ganin sun saɓa wa dokokinta na wa’azi.

Kafin dakatarwar, malamin ya kwashe kusan kwanaki 11 yana gabatar da tafsirin Ramadan na bana a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.

Bidiyoyin da suka tayar da kura

A kwanakin baya an fara ganin wasu bidiyoyin malamin suna yawo a shafukan sada zumunta. A cikin bidiyoyin, an ji shi yana sukar wasu shugabannin siyasa kan yadda suke tafiyar da harkokin tsaro a ƙasar.

A ɗaya daga cikin bidiyon, malamin ya ambaci sunayen wasu ministoci da gwamnoni da kuma manyan ‘yan siyasa, inda ya zarge su da gaza magance matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar Nijeriya.

Haka kuma a wani bidiyon, an ji malamin yana sukar Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, inda ya zarge shi da rashin ɗaukar matakan da suka dace domin magance matsalolin ƙasar.

Ra’ayoyi mabambanta

Dakatarwar ta janyo muhawara a tsakanin al’umma. Wasu na ganin matakin da Izala ta ɗauka ya dace, suna masu cewa hakan na iya taimakawa wajen dakile yadda wasu malamai ke mayar da wuraren tafsiri wajen tattauna siyasa ko kuma sukar juna.

Sai dai wasu kuma na goyon bayan malamin da aka dakatar. Su na ganin babu laifi idan malamin addini ya yi amfani da mimbarinsa wajen jawo hankalin masu mulki kan nauyin da ya rataya a wuyansu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Martanin malamin

Da yake magana da BBC Hausa, Sheikh Alƙali Zaria ya ce ya yi nadamar kalaman da suka janyo dakatarwar.

Ya kuma bayyana cewa ya karɓi matakin da aka ɗauka kansa da zuciya ɗaya, yana mai cewa hakan ba zai sa ya daina wa’azi da kira ga gyaran al’umma ba.

Yadda ake tsara tafsirin Ramadan

Gabanin watan Ramadan na bana, ƙungiyar Izala ƙarƙashin jagorancin Sani Yahya Jingir ta tura malamai 678 zuwa masallatai daban-daban a faɗin Nijeriya da kuma wasu ƙasashe maƙwabta domin gudanar da tafsirin Al-Qur’ani.

Tasirin malamai a al’umma

Masu nazarin al’amuran zamantakewa sun daɗe suna bayyana cewa malaman addini na da tasiri mai ƙarfi a cikin al’ummar arewacin Nijeriya. Wannan tasirin ya shafi harkokin addini da zamantakewa, har ma da siyasa.

A daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da damun ƙasar tsawon shekaru, wasu masana na ganin cewa muryoyin malamai na iya taka muhimmiyar rawa wajen jan hankalin gwamnati da al’umma kan muhimmancin samar da mafita.