Uwargidan shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira a ranar Laraba da a yi watsi da "al'adar jefar da kaya" ta hanyar amfani da kayayyaki sau ɗaya zuwa ga amfani mai ɗorewa da ya dogara kan kayayyaki masu inganci da ɗorewa.
Emine Erdogan, matar shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan kuma shugabar kwamitin ba da shawara ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya kan Kawar da Sharar Gida, ta yi jawabi a taron tattaunawa kan sauyin makamashi na na Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya.
Ta ce yanayin zafi da ya yi kamari, tiririn zafi, gobarar daji, ambaliyar ruwa, da guguwa mai tsanani sun zama ruwan dare game duniya, tana danganta su da ƙaruwar buƙatar makamashi da amfani da iskar gas mai yawa ke haifarwa.
"Bai kamata mu takaita batun sauya makamashi kawai ga tambayar ba: Ta yaya za mu iya samar da ƙarin makamashi mai tsafta? Ya kamata mu fara tunkarar batun ta hanyar tambaya: Me yasa dole ne mu samar da ƙarin makamashi?" in ji ta.
Ta yi tsokacin cewa mafita mai ɗorewa tana buƙatar magance tushen matsalar, tana mai lura da cewa makamashi, albarkatun ƙasa, da aikin ɗan adam na cikin kayayyakin da ake zubarwa daga ƙarshe.
Uwargidan shugaban ƙasa ta ba da misali da ɓarnar abinci a duniya, tana mai cewa ana ɓatar da abinci daidai da faranti tiriliyan 5.8 a kowace shekara kuma makamashin da ake amfani da shi wajen samarwa, kunshewa, shiryawa, adanawa, da rarraba shi shi ma ana asarar sa.
"Babbar damuwarmu ya kamata ta kasance mu guji al'adar jefar da kaya da ke tattare da kayayyakin da ake amfani da su sau ɗaya," in ji ta. "Don jin daɗinmu duka da kuma adalci tsakanin zamaninnika, dole ne mu koma ga al'adar amfani da kayayyaki masu ɗorewa ."
Erdogan ta ce za a iya tsara hanyoyin samar da kayayyaki don hana ɓarna kuma za a iya mayar da kayan da aka zubar zuwa kayan masarufi, tana kwatanta yanayi a matsayin abin koyi ga sake amfani da tarkacen kayayyaki.
Shirin Alkinta Shara na Turkiyya
Ta yi nuni da Shirin Alkinta Shara na Turkiyya, wanda aka ƙaddamar a shekarar 2017, a matsayin taswirar tsaron makamashi da albarkatu.
"Turkiyya na shirye-shiryen wannan sauyi ta hanyar hanzarta ayyukanmu na alkinta shara da saka hannun jari a makamashi mai tsafta," in ji ta.
"A yau, muna matsayi na biyar a Turai kuma na 11 a duniya dangane da ƙarfin makamashi mai sabuntawa da ke aiki," in ji ta. "Nan da shekarar 2035, muna da niyyar ƙara ƙarfin wutar lantarki ta hasken rana da iska da ake amfani da su zuwa megawat 120,000."
"Alkinta sharar gida ita ce hanya mafi ƙarfi da ke buɗe ƙofar zuwa ga canji na gaske a kowane fanni, daga samarwa zuwa amfani," in ji Erdogan.
Bayan jawabinta, an gudanar da taron tattaunawa tare da halartar mambobin majalisar ministocin Turkiyya da sauran jami'ai.




















