| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Gasar Kofin Duniya: Mexico ta zama ƙasa ta farko da ta tsallaka matakin sili ɗaya ƙwale
Mexico ta yi amfani da kurakuran da 'yan bayan Koriya Ta Kudu suka yi wajen kasancewa ƙasar da ta fara tsallakawa matakin sili ɗaya ƙwale a Gasar Cin Kofin Duniya.
Gasar Kofin Duniya: Mexico ta zama ƙasa ta farko da ta tsallaka matakin sili ɗaya ƙwale
Mexico za ta kara da Czech Republic ranar 24 ga watan Yuni a wasanta na ƙarshe a matakin rukuni. / Reuters

Ɗaya daga cikin ƙasashe masu masauƙin baƙi a Gasar Kofin Duniya ta 2026, Mexico, ta kai matakin sili ɗaya ƙwale a gasar bayan ta doke tawagar Koriya ta Kudu da ci 1-0 a filin wasa na Guadalajara mai cike da mutne da suke sowar goyon baya.

Ƙwallon da Luis Romo ya zura a raga bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ranar Alhamis ce ta sa Mexico zama ta ɗaya a rukunin A, yayin da take da sauran wasa ɗaya, sakamakon wani kuskuren gola.

‘Yan Koriya Ta Kudu sun kusa ramawa minti 87 da fara wasa a lokacin da golan Mexico Raul Rangel ya tare wata ƙwallon da Cho Gue-sung ya bugo daga kusa-kusa, sannan ya sake tare ƙwallon bayan an sake bugo ta, inda ya miƙa hannun damansa wajen hana ƙwallon wuce layi.

Mexico tana da maki shida daga wasanni biyu da ta buga a rukunin A, inda take gaba da Koriya Ta Kudu da maki uku yayin da take da maki biyar gaba da ƙasashen Czech Republic da Afirka Ta Kudu, waɗanda suka tashi da ci 1-1 ranar Alhamis a wasan da suka yi a Atlanta.

Tawagar El Tri na da ƙwallaye 3 kawo yanzu a cikin wasanninsu biyu kuma ba a zura mata ko ƙwallo ɗaya a raga ba.

Tawagogi biyu na sama a cikin ko wane rukuni za su wuce mataki na sili ɗaya ƙwale tare da tawagogi takwas da suka fi ƙarfi a cikin tawagogin da suka zama na uku a rukunoninsu.

A karon farko ana buga zagaye na 32 na wasanni a gasar cin kofin duniya bayan gasar ta faɗaɗa zuwa zuwa tawagogi 48.

Kocin Mexico Javier Aguirre ya yi canji uku daga tawagar da ta doke Afirka Ta Kudu da ci 2-0 a makon da ya gabata a wasan buɗe gasar.

Takwaransa, Hong Myung-bo, ya yi sauyi ɗaya , inda ya nuna amincewa da tawagar da ta taso daga ƙasa ta doke tawagar Czech Republic da ci 2-1.