Trump ya saka harajin kashi 25 kan ƙasashen da ke kasuwanci da Iran

Trump ya ce harajin na Amurka zai shafi duk wata ƙasa da ta ci gaba da ƙulla alaƙar kasuwanci da Tehran.

By
Trump ya ce harajin zai shafi kowace kasa da ta ci gaba da hulda da Iran. / AP

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa duk wata ƙasa da ke hulɗa da Iran za ta fuskanci harajin kashi 25 cikin 100 kan duk wata hulɗar kasuwanci da za ta yi da Amurka, yana mai cewa matakin zai fara aiki nan-take.

A cikin wata sanarwa, Trump ya ce harajin zai shafi kowace ƙasa da ta ci gaba da hulɗa da Iran.

"Daga yanzun nan, duk ƙasar da ta yi hulɗa da Iran za ta biya harajin kashi 25 cikin 100 kan kowane kasuwanci da ta yi da Amurka," in ji Trump.

Ya ƙara da cewa hukuncin zai shafi dukkan hulɗar kasuwanci da Washington, yana mai bayyana cewa ba za a bayar da wata togaciya ba.

Trump ya sake nanata barazanar a cikin sanarwa da dama, yana mai jaddada cewa ƙasashen da ke hulɗa da Iran za su fuskanci harajin a duk wata hulɗa da Amurka.

Sanarwar ta nuna ƙaruwar matsin lambar tattalin arziki ta Trump, yayin da yake alaƙanta damar shiga kasuwar Amurka da bin ƙa'idojin cinikayyar da ta shafi Iran.