| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Iran ta kai manyan hare-haren makami mai linzami da jirage marasa matuƙa a Gabas ta Tsakiya
Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran IRGC ta ce ta kai hari kan "sansanonin abokan gaba" a faɗin Bahrain da Kuwait da Jordan a matakin farko na harin ramuwar gayya kan Amurka, inda Tehran ta yi gargaɗin kai ƙarin hare-haren nan gaba.
Iran ta kai manyan hare-haren makami mai linzami da jirage marasa matuƙa a Gabas ta Tsakiya
Kafafen watsa labaran gwamnati na Iran sun ruwaito cewa IRGC ta kai hari filayen jirage biyu a Kuwait / Reuters

Sojojin Iran sun ƙaddamar da abin da kafafen watsa labaran gwamnati suka bayyana a matsayin babban harin makami mai linzami da jirage marasa matuƙa waɗanda suka faɗa kan “sansanonin abokan gaba” a faɗin Gabas ta Tsakiya, inda suka ƙona tankunan mai da ma'ajiyar harsasai a sansanin sojin sama na Prince Hassan a Jordan.

Rundanar Juyin Juya Halin Iran ta IRGC ta ce harin a kan wannan sansanin na Jordan shi ne mataki na farko na martaninta ga hare-haren Amurka kan sansanonin bakin teku na Iran, inda ta yi gargaɗin cewa za ta ci gaba kai hare-haren ramuwar gayya.

IRGC ta ce sojojin samanta sun kuma kai hari kan sansanin sojin sama na Sheikh Isa a Bahrain, inda ta ce ta kai hari kan wuraren gyaran helikwafta da garejin jiragen P-8 da cibiyar bayar da umarni da iko ta jiragen sama marasa matuka ta Amurka.

Masu AlakaTRT Afrika - Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran ta sanar da rufe Mashigar Ruwan Hormuz 'sai abin da hali ya yi'

Kafafen watsa labaran gwamnati na Iran sun ruwaito cewa IRGC ta kai hari filayen jirage biyu a Kuwait. Ikirarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin hare-haren ramuwar gayya tsakanin Iran da Amurka a faɗin yankin.

Ta ƙara da cewa ta kai harin ne bayan ta gano wuraren da kuma sa ido kan “motsin abokan gaba” a cikin awanni 48 da suka gabata.

A wata sanarwa, IRGC ta ce harin rundunar ta ruwa a cikin tashar Hormuz ya faɗa ne kan jirage biyu waɗanda ake zargi da kashe na’urar bin diddiginsu (tracker), karya ƙa'idojin zirga-zirgar ruwa da zama barazana ga tsaron ruwa.

"Halastaccen wuri na kai hari"

Hakan ya biyo bayan gargadin da Iran ta a yi ranar Litinin kan cewa duk wani wuri da aka yi amfani da shi wajen ƙaddamar da hare-hare kan kasar za a ɗauke shi a matsayin “halastaccen wuri na kai hari” don ramuwar gayya.

A wata sanarwa, Ma'aikatar Harkokin Wajen ta gargaɗi ƙasashen maƙwabta da su hana a yi amfani da yankunansu ko wuraren su na gwamnati da Amurka ko wasu ɓangarori wajen kai hari kan Iran.

Ta ce ƙasashen makwabta na da alhaki ƙarƙashin doka ta ƙasa da ƙasa hana a yi amfani da yankunansu wajen ayyukan soja kan Iran, tare da sake jaddada cewa “duk wani wurn da aka ƙaddamar” da hari zai zama wurinm da Iran za ta kai wa farmaki.

Wannan ci gaba ya zo ne bayan 'yan sa'o'i da rundunar sojin Amurka ta sanar da sabon zagaye na hare-hare kan Iran, inda ta ce aikin yana nufin rage ikon Tehran na kai hari kan jiragen ruwan kasuwanci a Mashigar Hormuz.

Ma'aikatar ta yi tir da hare-haren Amurka da aka kai a cikin awanni 22 da suka gabata, sannan ta bayyana su a matsayin babban take hakkin Kundin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ta zargi Washington da karya kusan dukkan sassa na yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a kwanaki 25 da suka wuce da kuma aikata “laifukan yaƙi” ta hanyar kai hari kan ababen more rayuwa na sufuri, kamun kifi, jiragen kaya da cibiyoyin nazarin yanayi.

Rumbun Labarai
Hari kan ɗaya daga cikinmu tamkar a kan dukanmu ne, in ji Turkiyya, Saudiyya da Pakistan
An kori manyan jami'an Hukumar Leken Asirin Isra'ila saboda gaza kifar da gwamnatin Iran
Iran da Oman sun amince kan hanyar gudanar da Mashigar Hormuz, in ji Tehran
Ministocin ƙasashen Larabawa da na Musulmai sun haɗu a Jordan don ɗaukar matsaya kan Gabashin Ƙudus
Yaƙin Iran na neman karar da makamai masu linzami na Amurka: rahoto
'Yansandan Dubai sun rufe shafukan sada zumunta 103 na bogi a ƙoƙarinsu na yaƙi da zamba
Trump ya buƙaci Iran ta ƙulla yarjejeniya da Amurka ko ta miƙa wuya
Shin za a amince cewa Netanyahu zai girmama yarjejeniyar janyewar Isra’ila baki daya daga Gaza?
Trump ya ce Amurka da Iran za su soma sabuwar tattaunawa a ranar Litinin
Pentagon ba ta da ƙarfin sojin ruwa na kare Isra'ila: Janar ɗin sojin Amurka
Saudiyya ta kammala shirye-shiryen kafa Ƙawancen Tsaron Teku tare da goyon bayan ƙasashe 14
Trump ya ce kwamitin sulhu na Gaza ya yarda Hamas ta ajiye makamai da janyewar Isra'ila daga yankin
Iran ta yi ikirarin lalata jiragen yaƙin F-35 na Amurka a Jordan
Amurka ta kai wa Iran sabbin hare-hare, in ji CENTCOM
Isra'ila ta kashe dala miliyan 46.5 wajen ƙoƙarin sa AI ya yaɗa ra'ayoyinta kan yaƙin Gaza
Amurka da Saudiyya sun kai hari kan ƙungiyar da ke goyon bayan Iran a Iraki
Iran ta ce babu kyakkyawan yanayin da ya dace ta tattauna da Amurka duk da suna musayar saƙonni
Trump ya dakatar da kai wa Iran hari saboda karancin makaman tsaron samaniya — rahoto
An kai wa ma'aikatan jiragen ruwan India hari kusa da mashigar Hormuz
Iran ta yi watsi da tayin tsagaita wuta da Amurka ta yi mata - rahoto