Sojojin Amurka sun kwashe wasu jiragen sama daga sansanin soji na biyu a Birtaniya, biyo bayan wata barazanar da ake zargin ta fito daga Iran, a cewar rahoton jaridar Wall Street Journal a ranar Litinin.
Wasu jiragen sama biyu na dakon mai da ke aiki daga sansanin RAF Mildenhall sun karkata zuwa Jamus da safiyar Litinin, yayin da kuma aka kwashe wasu jiragen da dama daga sansanin zuwa Jamus da wasu wurare, in ji rahoton.
Jaridar ta ce har yanzu jami'an Amurka na tattaunawa kan hakikanin yanayi da kuma cikakken bayani game da barazanar da aka ruwaito.
Kakakin Ma'aikatar Tsaron Birtaniya ya ki yin karin bayani kan rahoton barazanar, inda ya ce: “Ba mu cika yin tsokaci kan ayyukan wasu kasashe ba. Jiragen sama da sauran kayan aikin soji na sauya wurare akai-akai bisa bukatun ayyukan soja,” in ji shi.
Wani lamari na tsaro ya jawo janye jiragen yakin Amurka a baya
Wannan mataki ya zo ne makonni kadan bayan kama wasu 'yan Birtaniya biyar a watan Satumba a wajen sansanin sojin sama na RAF Fairford da ke kudu maso yammacin Ingila.
Bayan wannan lamari, sojojin Amurka sun janye jiragen yakin B-1 daga sansanin saboda dalilai na tsaro.
A baya, Amurka ta rika amfani da sansanin RAF Fairford wajen kai hare-haren jiragen yakin sama kan Iran.



















