Rundunar sojin Jamus na fama da wani mummunan bincike na cikin gida, bayan da sabbin bayanai na ma'aikatar da aka gano suka nuna kusan jami’a 2,000 da ake zargi da aikata laifukan lalata a cikin shekaru biyar kacal.
Alkaluman, wanda Der Spiegel suka fara bayar da rahoto, sun fallasa wani yanayi mai tayar da hankali da ke ɓoye a cikin rundunonin sojojin.
A cewar tsarin rahotannin cikin gida na Ma'aikatar Tsaro, korafe-korafe sun karu daga 312 a shekarar 2021 zuwa 472 a shekarar 2025.
A cewar rahoton, jami'ai sun ce karuwar na iya nuna dduwar sha'awar wadanda abin ya shafa na fitowa fili, maimakon kara tabarbarewar hali kawai.
Duk da haka, wannan adadi ya tsoratar da masu sanya idanu, inda rahotanni 1,114 kacal daga cikin kusan 2,000 ne aka taba turawa ga masu gabatar da kara.
Cin zarafin mata ya fi kowanne yawa a cikin zarge-zargen, inda aka samu rahotannin abubuwan da suka faru guda 828 a cikin tsawon shekaru biyar na rahoton.
Fiye da zargin yin lalata guda 50 da aka yi sun shafi cin zarafin yara, a cewar takaitaccen bayanin laifukan da ma'aikatar tsaro ta fitar.
An kuma danganta karin lalata sama da 200 da suka shafi batsa da yara, yayin da aka bayar da rahoton yin kallo a lokuta 31 daban-daban.
Masu bincike sun kuma rubuta rahotanni 395 na zargin cin zarafin mata, tilastawa ko fyade a cikin rundunar soji.
An bayyana zargin cin zarafin mata sau biyu a cikin alkaluman da ke tayar da hankali, kodayake ma'aikatar ba ta tabbatar da wani hukunci da aka yanke musu ba.
’Alkaluman da yawa’
Sufeto Janar na Bundeswehr Carsten Breuer ya karya shirun da ya yi a wannan makon, yana bayar da gargaɗin da ba a saba gani ba kuma na musamman.
"Adadin afkuwar lalatar da aka rawaito ya yi yawa," Breuer ya shaida wa sojoji da kwamandoji a cikin umarnin cikin gida da ya fitar.
Ya yi gargaɗin cewa, "Irin wannan rashin da'a," ba dole ba ne "manya, ma'aikata, ko daidaikun mutane" su "karɓi shi" a cikin kowace runduna.
"Ko da kuwa da gangan suke kallon wani abu ko kuma suna jure wa irin waɗannan abubuwan da suka faru ba tare da wata damuwa ba dole ne ya haifar da sakamako," in ji Breuer.
Kimanin jami’ai 267,000 ne ke hidima a rundunar sojin Jamus ko ayyukan farar hula a rundunar, inda mata suka ƙunshi kashi 13 cikin ɗari na sojojin.
A cewar wani rahoto, cin zarafin mata, wanda wani lokacin manyan sojoji ke yi, yana faruwa akai-akai a cikin barikokin sojojin Jamus.
‘Bakaken alkaluma’
Masu bincike yanzu sun yi gargadin cewa ainihin girman cin zarafi zai iya wuce waɗannan alkaluman na hukuma da babban gibi.
Cibiyar Tarihin Soja da Kimiyyar Zamantakewa ta Sojojin Jamus yanzu tana gudanar da bincike kan zargin rashin bayar da rahoto, wanda aka yi wa lakabi da "binciken duhu."
Ana sa ran gano abubuwan da aka gano na farko daga wannan binciken kafin ƙarshen wannan shekarar.


















