Jirgi maras matuƙi na Isra'ila ya kashe Falasɗinawa duk da an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta

Ma’aikatan Asibitin Al Shifa na birnin Gaza sun karɓi gawawwakin maza biyu da kuma wasu Falasdinawa biyu da suka jikkata bayan harin, wanda majiyoyin likitoci suka ce jirgi maras matuƙi na Isra’ila mai ƙafa huɗu ne ya kai harin.

By
Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a Gaza / Reuters

Harin jirgi maras matuƙi na Isra’ila ya kashe Falasdinawa biyu ya kuma jikkata wasu biyu a safiyar Asabar a yankin Al Atatra na Beit Lahiya a arewacin Gaza, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma kusan watanni biyu da suka wuce, in ji majiyoyin likitoci ga Anadolu.
Ma’aikatan Asibitin Al Shifa na birnin Gaza sun karɓi gawawwakin maza biyu da kuma wasu Falasdinawa biyu da suka jikkata bayan harin, wanda majiyoyin likitoci suka ce jirgi maras matuƙi na Isra’ila mai ƙafa huɗu ne ya kai harin.

A wani lamari na daban, hukumar kare fararen hula Kariya ta Gaza ta ce wani hari na Isra’ila ya kashe wani ma’aikacinta, Suhail Abdullah Dahman, da yammacin Jumma’a, ya kuma jikkata ɗansa sosai yayin da suke kan hanyarsu ta duba gidansu a Beit Lahiya, wanda wuri ne wanda ba shi ƙarƙashin ikon Isra’ila.

Hukumar ta ce mutuwar Dahman ta ƙara adadin ma’aikatan kare farar hula da aka kashe tun daga Oktoban 2023 zuwa 142.

Da safiyar Asabar, dakarun Isra’ila sun kaddamar da jerin munanan hare-haren sama tare da rusa gine-gine a yankuna daban-daban da suke ƙarƙashin ikonsu a Gaza, alamar sabuwar keta yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiwatarwa a mataki na farko ranar 10 ga Oktoba.

Sojojin Isra’ila na ci gaba da riƙe ikon hanyar kudu da gabashin Gaza, tare da manyan sassa na arewa, wanda ke kaiwa fiye da kashi 50 cikin 100 na yankin gaba ɗaya.

Isra’ila na ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar da ta sanyawa hannu da Hamas, inda ta keta yarjejeniyar fiye da sau 100 tare da kashe Falasdinawa 366 har zuwa ranar Alhamis, a cewar hukumomin Gaza